✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid ta taya Mbappe Naira Tiriliyan 1 da rabi

Rahotanni sun ce kulob din Real Madrid da ke Spain ya taya dan kwallon kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa Kylian Mbappe…

Rahotanni sun ce kulob din Real Madrid da ke Spain ya taya dan kwallon kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa Kylian Mbappe a kan Fam miliyan 340 (kimanin Naira tiriliyan daya da biliyan 574 da miliyan 20).

Idan cinikin ya kullu, Mbappe zai kasance dan kwallo mafi tsada a duniya a tarihi.  Wanda ke rike da wannan kambi shi ne dan kwallon Brazil Neymar wanda kulob din PSG ya sayo daga FC Barcelona na Spain a kan Fam miliyan 200 kimanin shekara hudu da suka wuce.

Rahoton da kafar labarai ta NaijaNews ta kalato ya nuna kulob din Madrid ya dade yana zawarcin Mbappe kuma alamu sun nuna zai amince da wannan tayi.

Kocin Madrid Zinedine Zidane yana sha’awar sayo dan kwallon  kafin karshen kakar wasa ta bana.

Yanzu dai masu sha’awar kallon kwallon kafa sun zuba ido su ga yadda cinikin zai kaya musamman magoya bayan kulob din Madrid.