Da Dumi Dumi

Mafi karancin albashin Najeriya bai kai abin da ake kashe wa fursunan Amurka kullum ba – Bincike

Ministan cikin gida, Ra’uf Aregbesola
Ministan cikin gida, Ra’uf Aregbesola

A kwanakin baya ne aka samu labarin cewa mafi karancin albashin da ake gogoriyon biyan ma’aikatan Najeriya na Naira dubu 30 bai kai abin da ake kashe wa fursuna a kasar Amurka ba.

An samu wadannan labarai ne a wasu daga cikin jaridun kasar nan, wanda kuma ake danganta labarin ga Ministan Harkokin Cikin Gida Ra’uf Aregbesola, lamarin da ya tayar da kura a dandalin sada zumunta na zamani.

Yadda rahoton yake

Rahoton wanda jaridar The Punch ta wallafa a ranar 19 ga Oktoba, ya ce, “Ministan Cikin gida, Ra’uf Aregbesola, a ranar Juma’ar da ta gabata ya ce a duk rana ana kashe wa wanda ake tsare da shi a gidan yari Naira dubu 31,000 a kasar Amurka.”

Ya ce kudin ya dara wanda Gwamnatin Tarayya ta kayyade a matsayin albashi mafi karanci ga ma’aikatan Najeriya na Naira 30,000.

ADVERTISEMENT

Ya ce ma’aikatarsa za ta duba yiwuwar fara ciyar da kowane daurarre a kan Naira 730 a matsayin kudin abincin kuwace rana a shekarar 2020.

Rahoton ya sake ruwaito Aregbesola yana cewa “Gwamnatin Amurka ta kasafta kudin da ya kai Dala biliyan 81 ga Hukumar Gyaran Tarbiyya a bara.

“A duk rana kowane fursuna yana amfana da tsakanin Naira 31,000 zuwa 61,000 a kasar  Amurka.

Kudin da ake kashe wa fursuna a kasar Amurka a kullum, ya fi sabon mafi karancin albashi na Naira dubu 30 da ake sa ran biya ga ma’aikatan Najeriya.”

Bin diddigi

Binciken da Aminiya ta yi ranar Lahadin da ta gabata a kan hasashen Ministan dangane da kudin da ake kashe fursunan Amurka duk rana cewa ya haura sabon albashin Naira dubu 30 da za a fara biyan ma’ikata a Najeriya duk wata, ta gano cewa batun haka yake, amma akwai kuskure a kididdigar da Ministan ya ambata, domin kudaden sun haura hasashen Ministan.

Wata jaridar Birtaniya mai suna Mail  Online  ta wallafa wani rahoto ranar 25 ga Oktoban bara cewa “Jihar Kalifoniya tana kashe Dala biliyan 8.6 duk shekara a gidajen yarinta wanda ya dara na kowace jiha a Amurka, inda kowane fursuna ana kiyasin kashe masa Dala dubu 64 da 642.”

Yawan fursunonin da ke gidan yarin Kalifoniya ya kai dubu 133 da 40, kuma ana kashe wa duk mutum daya da ke gidan yarin Dala 177.10 (kimanin Naira dubu 63 da 756), bisa canjin Dala daya kan Naira 360.

Haka binciken Aminiya ya ga wani rahoton da ke kunshe a takardun Hukumar Kula da Shari’a ta Amurka, wanda ya bayyana cewa mafi karancin abin da ake kashe wa fursuna a gidajen yarin kasar a kasafin bana, shi ne Dala biliyan 7.141 a kan fursunonin 180,210.

Idan aka ware wa kowane fursuna kudi a cikin kasafin, zai kama Dala dubu 39 da 626 (kimanin  Naira miliyan 14da dubu 265 da 360), duk shekara. Sannan duk rana zai kama Dala 108.56 (kimanin Naira dubu 39 da 81da kwabo 60) kan canjin Dala a Naira 350.

Jihar New York ce ta fi kowace jiha a Amurka yawan gidajen yari, kuma a bana ta kasafta Dala biliyan 3.295 ga daukacin gidajen yarin jihar guda 52 wanda suke da yawan ’yan fursuna dubu 45 da 363.

Idan aka ware wa kowane fursuna abin da zai amfana da shi, shi ne  Dala dubu 72 da 636 da 29 (kimanin Naira miliyan 26 da dubu 149 da 64). duk shekara, a kullum kuma zai amfana da Dala 199 (kimanin  Naira dubu 71da 640).

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya