Da Dumi Dumi

Magajiya Dambatta: Daga  mabaraciya zuwa miloniya

Magajiya Dambatta
Magajiya Dambatta

Rayuwar tsohuwar mawakiya Magajiya Danbatta ta kasance cike da darasi mai yawa.

Magajiya Dambatta, wadda asalin sunanta Halima Malam Lasan, an haife ta ce kimanin shekara 84 da suka gabata, kuma ta yi tashe da shahara sosai, inda ta kasance cikin mawaka manya da duniyar Hausa ke sauraro kuma suka yi takama da su a tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980.

Bayan dogon lokaci tana tashe, sai kwatsam ta yi batar dabo, inda aka daina jin duriyarta, wadanda suka santa kuma suka manta da ita, matasa kuma da ma can ba su santa ba.

Kamar yadda ta bayyana a tattaunawarta da Aminiya, ta fara waka ce tun tana da shekara 12, kuma ta yi wakoki da dama inda ta shahara a wancan lokaci ta yadda idan ba ta je taro ta yi waka ba, taron bai cika yin dadi ba. Ta ce  sun hadu da Shata a lokacin  bikin cikar Gidan Rediyon Najeriya Kaduna shekara 30, inda ta rera wakarta mai suna Soriyal.

Yadda aka gano Magajiya Dambatta

ADVERTISEMENT

Bayan dogon lokaci, sai kwatsam a ranar 23 ga Disamban bara, dan jarida Jafar Jafar ya wallafa wani faifan bidiyo na Magajiya Dambatta na wakar da ta yi a Gidan Rediyon Najeriya  Kaduna na bikin cika shekara 30.

A kasan bidiyo, Jafar Jafar ya rubuta a shafinsa na facebook da Ingilishi cewa, “Ku nishadantu da zakin muryar zabiya Magajiya Dambatta. Ina fata za ku ji dadin karshen mako.”

Wannan bidiyon da ya wallafa, ya yi fice cikin sauri, inda mutane da dama suka rika tuna lokacin da mawakiyar ke tashe, wadansu kuma suka rika tuna lokacin da Gidan Rediyon Najeriya na Kaduna ke yawan sanya wakarta. An yada faifan bidiyon daga shafin Jafar Jafar na facebook sau 629, sannan an yi martani a kan rubutun sau 142.

Daga cikin wadanda faifan bidiyon ya burge su, wadansu sun san ta, wadansu sun ji labarinta, wadansu sun ji wakarta, wadansu kuma lokacin suka santa. Amma daga cikinsu akwai Munzaili Hausawa wanda baya ga saninta da ya yi, yana da labarin inda take, wanda shi ne silar gano ta.

Jafar Jafar ya sake wallafa rubutu a shafinsa na facebook a ranar 23 ga Disamban cewa, na hadu da Magajiya Dambatta mai shekara 84 a gidanta da ke Makoda a Jihar Kano. Bayan na wallafa tsohon faifan bidiyonta, wani abokina da ke aiki a Gidan Rediyon Kano, Munzali Hausawa ya sanar da ni cewa tana raye.

“Wannan ya sa na tuka mota na tsawon kilomita 70 domin ganinta cikin tsufa. Magajiya wadda yanzu makauniya ce ta bayyana mini yadda take rayuwa da abin da ta samu ta hanyar bara a kauye. Zakin muryarta yanzu ya fara dushewa, amma ta rera min wasu daga cikin fitattun wakokinta. Babban makadinta da mai biye masa, (Dan Kuntukuru) duk sun rasu, amma yawancin masu amshi wadanda a lokacin matasa ne suna raye,” inji shi.

Jafar Jafar ya kara da cewa, “Kamar yadda wani rubutu da aka yi  game da wakokinta, wanda tsohon Manajan Daraktan Gidan Rediyo Kano, Adamu Salihu ya rubuta, wata wakar wayar da kan mutane a kan muhimmancin sanya yara a makaranta da ta yi a shekarun 1970 ta taimaka wajen sanya yara sama da 3000 a makaranta. Ina tsammanin daga cikin yaran da a lokacin iyayensu suka sanya a makarantar a wancan lokacin yanzu wadansu sun zama farfesoshi.

“Amma ita Magajiya tana rayuwa cikin talauci mai tsanani. A Najeriya haka mutum ke yin tashe, sannan ya fado kasa kamar ba a yi shi ba,” inji shi.

Lokacin da ake karrama Jafar Jafar
Lokacin da ake karrama Jafar Jafar

Ma’anar Soriyal

A wani faifan bidiyo da Jafar Jafar ya saka, an tambaye ta ma’anar Soriyal da ta ambata a wakarta, sai ta ce, “Daurin kallabin da nake yi. Ka san lokacin gyauto nake daurawa, sannan ga jakata, sannan ga mai barewa. Lokacin mai barewa.” Har ta ce ko za a dauko mata gyauton kallabi ta yi daurin.

 

Yadda aka tara mata sama da Naira miliyan 5

Bayan Jafar Jafar ya wallafa wannan rubutu na biyu, rubutun ya yi yawo matuka, inda kusan mutum 1,100 suka yi martani a kan rubutun, sannan 2,800 suka yada shi. Daga cikin masu sharhi ne suka rika cewa ya kamata a tallafa mata, wadansu ma har suka fara daukar alkawarin bayar da gudunmawa.

Daga cikinsu, Dokta Ibrahim Musa ya bada shawarar cewa za a iya tara Naira miliyan  domin tallafa mata. Bayan nan ne a ranar 23 ga Disamban, Jafar Jafar ya sake cewa ana ta kiransa a waya cewa ya kamata a tallafa mata ta hanyar tara mata kudi.

Ya ce, “Fitaccen ma’aikacin taimako da ya kwashe sama da shekara 20 a harkokin jinkai, Musa Abdullahi Sufi ya ce zai bayar da asusun ajiyar wata gidauniyar da yake cikin Kwamitin Amintattunta, sannan zai rika ba Dokta Ibrahim Musa da ni (Jafar Jafar) bayanai kan yadda ake ciki na tallafin da ake samu. Ni kuma zan rika bayyana wa mutane yadda ake ciki. Burinmu shi ne mu sake gina mata gida, mu saya mata kayan sawa da abinci. Bari mu ga yadda abin zai kasance.” Sai ya sanya asusun ajiyar da za a rika tura kudin.

Cikin kwana uku aka tara kudin da aka yi mamaki, inda a ranar farko mutum 43 suka tara Naira dubu 402 da 300. sannan zuwa rana ta uku, mutum 367 sun tara Naira miliyan 2 da dubu 921 da 100, kamar yadda Ibrahim Sanyi-Sanyi ya wallafa a shafinsa.

A karshe Jafar Jafar ya ce an tara Naira miliyan 5 da dbu 6 da 222, sannan ya  ce sun je gidan tsohuwar mawakiyar, sun tattauna da ’yan uwanta da makwabta da dattawan gari kan yadda za su tallafi rayuwarta.

Ya ce, “Bayan mun je gidanta ni da Musa Abdullahi Sufi da Ibrahim Sanyi-Sanyi da Munzali Hausawa, mun bayyana mata nasarar da aka samu wajen tara kudi. Ta yi godiya gare mu da kuma wadanda suka tara kudin. Sannan ta tabbatar mana cewa ta daina bara.

Tuni Dokta Kabir Abdussalam ya duba idonta. Za a kai ta Asibitin Koyarwa na Aminu Kano domin duba lafiyarta. Muna fata idonta zai bude bayan an yi mata tiyata.

“Tuni mun sanya ejan ya nemo mana gida ko fili a kauyen da za mu gina mata gida ko mu saya. Wasu daga cikin kudin da aka tara za mu yi amfani da su wajen saya ko gina mata gida,” inji shi.

 

Yadda za a dauki nauyin kula da ita na shekara uku

  1. Za a rika ba ta kudin kashewa Naira dubu 15 duk wata, inda za a rika ba ta Naira dubu 5 duk kwana 10. Wa ita za a rika kudin kai-tsaye. Ya kama Naira 180,000 ke nan duk shekara.
  2. Za a rika ba ta Naira dubu 15 a duk rubu’in shekara domin sayen sabulu da man shafawa da turare. Shi ma Naira dubu 5 ke nan duk wata baya ga na kashewa da za a rika ba ta. Ya kama Naira dubu 60 ke nan a shekara.
  3. Za a rika ba ta Naira dubu 40 kudin kayan Sallah a shekara. Dubu 20 ke nan kowace Sallah. Za a rika ba ta wannan kudi ne duk kusa da Sallah baya ga na kashewa da kayan bukata.
  4. Za a rika ba ta kudin abinci na Naira dubu 12 duk wata. Za a rika ba jikanta wanda yake ciyar da ita. Naira dubu 144 ke nan a shekara baya ga na kashewa da kayan bukata.
  5. Za a rika biyanta Naira dubu 5 duk wata domin kula da lafiyarta. Naira dubu 60 ke nan a shekara.
  6. Za a rika ba ’yar jagorarta Naira dubu 3 kudin kashewa a makaranta duk wata. Naira 100 kullum. Za a rika ba mahaifiyar ’yar jagorar Naira dubu 36 ke nan a shekara.

Jimilla zai kama Naira dubu 520, wanda zai kama Naira miliyan 1 da dubu 560.

 

An karrama Jafar Jafar bisa kokarinsa

Gidauniyar Grassroot Care and Aid Foundation (GCAF) ta karrama Jafar Jafar a matsayin Gwarzon Shekara shi da sauran wadanda suka taimaka wajen tabbatar da tallafin. Shugaban Kungiyar, Ambasada Auwal Muhammad Danlarabawa ya ce, “Muna alfahari da ayyukan alheri na wadannan bayin Allah a wannan gagarumin aiki da suka yi wato Jafar Jafar da Musa Abdullahi Sufi da Ibrahim Sanyi-Sanyi da kuma Dokta namu. Wannan gangami da aka yi na taimaka wa Malama Magajiya Dambatta abin yabawa ne kwarai da gaske, mun yi farin ciki. Don haka ne wannan gidauniya ta yaba musu da shaidar karramawa ta Gwarazan Shekarar 2019 a wannan rana da addu’ar Allah Ya kara dafa musu a wannan kokari ya zama ya dore.”

Haka ma marubuci Tunde Asaju ya bayyana Jafar Jafar a matsayin Gwarzon Dan Jaridarsa na 2019, bisa kokarin da ya yi na ceto rayuwar Magajiya Dambatta.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya