✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maganin Gargajiya Ya Kashe Mutum 2, Wani Na Asibiti A Ondo

Wasu matasa biyu da suka je bikin al’ada kauyen Ipe Akoko a Karamar Hukumar Akoko ta Kudu maso Gabas a Jihar Ondo sun sheka barzahu…

Wasu matasa biyu da suka je bikin al’ada kauyen Ipe Akoko a Karamar Hukumar Akoko ta Kudu maso Gabas a Jihar Ondo sun sheka barzahu bayan sun sha wani maganin gargajiya.

Matasan, Alex Ojulewa da Samuel Alonge sun kece da amai bayan sun sha maganin da wata mata ta jika a cikin garin ranar Lahadi.

Wani da abin ya faru a gabansa sai da ya bukaci mu sakaya sunansa, ya bayyana cewa matasan biyu sun zo ne domin halartar wani biki da aka fi sani da “Ibogbe” a yankin a lokacin da lamarin ya faru.

Ya bayyana cewa wani mutum mai suna Adu Johnson, wanda shi ma ya sha jikon yana a sibiti inda a halin yanzu yake kwance rai a hannun Allah.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace an fara bincike kan yadda abin ya faru domin daukar matakin da ya dace.