Da Dumi Dumi

Magidanci ya kashe ‘ya’yansa biyu a Ebonyi

Ana zargin wani magidanci mai suna Chinasa Ogbaga, wanda ya fito daga al’ummar Egwuagu Okpuitumo da ke Karamar Hukumar Abakaliki a Jihar Ebonyi da yanka ’ya’yansa biyu yayin da kuma ya yi kusa guntile kan daya. Wanda ake zargi kamar yadda wakilin Aminiya ya samu labari sai da ya bari an kwanta barci da daddare ya faki idon jama’a da na makwabta ya tafi da yaran cikin daji ya aikata abin da ake zarginsa.

Yaran da mahaifin nasu ya yi wa yankan rago su ne Chikamso Ogbaga, dan shekara shida sai kuma Chizaram Ogbaga mai shekara hudu. Wanda yake da sauran shan ruwa da ya kubuta shi ne Emmanuel Ogbaga, dan shekara biyu wanda wasu da suka ji kukan yaron suka garzayo suka kawo masa dauki suka kubutar da shi.

An kwantar da Emmanuel a Asibitin Koyarwa na Aled Ekweme, ana jinyarsa.

Mahaifiyar wanda ake zargi da kashe ’Ya’yan nasa Uwargida Ogbaga, ta shaida wa wakilinmu cewa, “Ya rabu da mahaifiyar yaran ne a farkon bana, kuma yana zaune kalau da yaran ban san abin da ya kai shi ga aikata hakan ba.” Cikin kwalla ta tabbatar da cewa “Shi ne yake daukar dawainiyar biyan kudin makarantar yaran tun daga garin Anacha a Jihar Anambra inda yake gudanar da harkokin kasuwancinsa yake barowa domin ya zo ya biya wa yaran kudin makaranta.

Mahaifiyar, ta danganta kisan kai da danta ya yi da cewa sharrin Shaidan ne.

ADVERTISEMENT

 

 

Share