✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magungunan gargajiya za su yi kafada da kafada da na Bature – Dokta Maigida Kachako

An bayyana cewa nan gaba kadan magungunan gargajiya za su yi kafada da kafada da na Bature duba da samun makaranta sukutum da ke koyar…

An bayyana cewa nan gaba kadan magungunan gargajiya za su yi kafada da kafada da na Bature duba da samun makaranta sukutum da ke koyar da sha’anin magunguna gargajiya a fadin Jihar Kano.

Wannan bayani ya fito daga Shugaban Makaranatar Harkokin Maganin Gargajiya da ke Jihar Kano (KITMER) Dokta Yakubu Maigida Kachako lokacin da yake jawabi awajen taron kara wa juna sani mai taken ‘maraba da Ramadan ‘ da Makarantar Koyar da Harkar Maganin gargajiya (KITMER) ta shirya a Kano.

Ya bayyana cewa an shirya taron ne don daliban makaranar su nuna wa al’umma irin abubwuan da suke koya a makaranatar tare da janyo hankulan al’umma su san cewa yanzu maganin gargajiya ya wuce inda ake tunani.

Da yake bayani game da dalilin bude makarantar da aka fara bara, Dokta Kachako ya bayyana cewa da samuwar makaranatar harkar maganin gargajiya za ta inganta a jihar da kuma kasa baki daya domin tsarin makaranatar yana da alaka da na tsarin koyar da aikin likitanci.

“Idan kin kula dalibanmu suna amfani da kayan makaranta da yawancin ake amfani da su a makarantun boko. Muna so ya kasance mai maganin gargajiya zai iya bude asibiti. Muna so a wai gari mai maganin gargahiya zai gwada mara lafiya. Muna kuma burin mu ganin cewa masu magungunan gargajiya sun zama kwararu a fani ka daban-daban, misali a sami wani ya kware a bangaren ido wani kunne da sauransu. Idan har muka samu haka to na tabbata Najeriya za mu yi kafada da kafada da sauran kasashen da suka yi fice a harkar maganin gargajiya kamar China da Indiya da sauransu.”

Dokta Kachako ya yi kira ga gwamnati da ta dauki nauyin masu harkar maganin gargajiya don  samun ilimi a wannan makarantar, a cewarsa hakan zai sa a samu tsari mai  tsafta a cikin harkar.