Da Dumi Dumi

Yayan mahaifin gwamnan Sakkwato ya rasu

Shaikh Haruna Waziri Usman, yayan mahaifin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya rasu ranar Alhamis

Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi rashin kawunsa ranar  Alhamis, 7 ga watan Mayu, bayan ya shafe shekaru 96 a duniya.

Marigayin, Shaikh Haruna Waziri Usman yaya ne ga mahaifin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yada labarai Muhammad Bello ne ya fitar da sanarwar rasuwar.

Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne a gidansa da ke garin Tambuwal.

Marigayin, wanda aka fi sani da Shehi, shi ne jagoran darikar Tijjaniya a garin Tambuwal gaba daya.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya