✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifin Iheanacho ya sanya masa farashin Naira miliyan 200

Duk kulob din da ke bukatar daukar Kelechi Iheanacho, daya daga cikin ’yan kwallon da suka fafata a gasar cin kofin duniya na matasa da…

Duk kulob din da ke bukatar daukar Kelechi Iheanacho, daya daga cikin ’yan kwallon da suka fafata a gasar cin kofin duniya na matasa da ya gudana a Dubai sai ya ajiye zunzurutun Yuro miliyan daya, kwatankwacin Naira miliyan 200.

Wannan kalami ya fito ne daga bakin mahaifin Kelechi Iheanacho jim kadan bayan Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi wa ’yan wasan da jami’ansu goma ta arziki bayan nasarar lashe kofin duniya na matasa karo na hudu a karshen makon jiya.
Kelechi Iheanacho ne ya zura kwallaye shida a raga da hakan ta sa ya kasance na biyu a cikin ’yan kwallon da suka fi zura kwallo a raga a yayin gasar.
Kafar sadarwar MTNfootball.com ta kalato cewa mahaifin dan kwallon tuni ya shaida wa duniya cewa duk kulob din da ke bukarar dansa ya buga masa kwallo sai ya ajiye Yuro miliyan daya, kwatankwacin Naira miliyan 200.
Tuni kulob din FC Porto da ke Fotugal ya ajiye zunzurutun Yuro dubu 250 kwatankwacin Naira miliyan 56 amma mahaifin ya yi kememe ya ce dan nasa ba zai sanya musu hannu ba.
Akalla ejen-ejen bakwai ne suka nemi dan kwallon da ya amince su zame masa dillalan cinikinsa don sayar da shi ga kulob din da ya dace da shi. Kuma sun cimma matsaya cewa kowane daga cikinsu zai samu kaso a duk lokacin da cinikin dan kwallo ta kaya.