Da Dumi Dumi

Mahaifin Jarumi Nura Hussaini ya rasu

Jarimi Nura Hussaini
Allah Ya yi wa mahaifin fitaccen jarumin Kannywood, Nura Hussaini Malam Hussein rasuwa.
Da yake sanar da rasuwar, jarumi Baballe Hayatu ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Allah Ya yi wa malam Hussain rasuwa, mahaifi ne ga dan uwa kuma abokina Nura Husseini.”
Manyan jarumai na masana’antar Kannywood ciki har da Ali Nuhu da Baballe Hayatu da Rukayya Dawayya da sauransu ne suka nuna jimami da ta’aziya a kan rasuwar mahaifin abokin sana’ar su, Nura Hussaini.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya