✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu sun sace matan aure

‘Yan bindiga sun harbe Babban Baturen ‘Yan Sanda na Babban Ofishin ‘Yan Sanda na Gidan Madi da ke Karamar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato. Maharan…

‘Yan bindiga sun harbe Babban Baturen ‘Yan Sanda na Babban Ofishin ‘Yan Sanda na Gidan Madi da ke Karamar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato.

Maharan sun kuma kashe wani hafsan dan sanda a ofishin suka kuma yi garkuwa da matan biyu na wani fitaccen mutun a yankin.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato, ASP Muhammad Sadiq ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa “Tabbas an kai hari na babu gaira babu dalili a Hedikwatar ‘Yan Sanda da ke Gidan Madi a cikin dare.

“Ina ba da shawara a dakaci karin bayani bayan mun kammala binciken da tuni Kwamishinan ‘Yan Sanda ya umarci a gudanar kuma a yanzu haka yake wurin da abin ya faru”.

Wasu shaidu sun ce ‘yan bindigar sun yi wa ‘yan sandan kwanton bauna ne suka kashe su a lokacin da jami’an ke kokarin ceto matan da aka yi garkuwa da su a tsakar daren Alhamis. 

Wasu rahotanni kuma na cewa na cewa sai da ‘yan bindigar suka kai wa Babban Ofishin ‘Yan Sandan hari suka kashe hafsoshin suka dauke bindigoginsu kafin suka yi garkuwa da matayen.