✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai safarar mata zuwa Italiya ta shiga hannu

Hukumar Shigi da Fici ta Kasa a Jihar Kano ta ce ta kama mata takwas wadanda wata mata ke kokarin safararsu zuwa kasar Italiya. Kwamandan…

Hukumar Shigi da Fici ta Kasa a Jihar Kano ta ce ta kama mata takwas wadanda wata mata ke kokarin safararsu zuwa kasar Italiya.

Kwamandan Hukumar a Kano, Isiak Yusuf ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar wa manema labarai wadda ake zargi mai suna suna Misis Sweet Okoye.

Ana zargin Misis Okoye ta dauko matan ne daga garin Benin a Jihar Edo da niyyar ketarewa da su zuwa kasar Italiya ta iyakar Jamhuriyyar Nijar.

Shugaban Hukumar ya ce lokacin da ake bincike, hukumar ta gano cewa wadanda ake kokarin safarar tasu, wadanda shekarunsu suka kama daga 19 zuwa 30, sun bayar da Naira dubu 30 zuwa dubu 300 a matsayin kudin sufurinsu.

An bayyaan sunayen matan da hukumar ta tserar da Lobeth Shigie da Esther Sunday da Doris Omorure da Mary Eneguma da Sophia Ujiagbe da Gloria Abraham Nkia da Fabour Roland.

Sai dai Mista Isiak ya ce matan ba su ba hukumar hadin kai lura da yadda suke kokarin boye bayanai masu muhimmanci wadanda watakila hakan ya faru ne bisa yarjejniyar da suka kulla da wacce ake zargin.

“Wadansu daga ciki sun dage cewa wai za su je Nijar ne don haduwa da mazansu, sai dai sun gaza gano mai yi musu jagorar a Kano. Sai dai kuma matar da ta yi safarar tasu tuni ta amsa laifinta,” inji shi.

Da yake bayani a kan matakin da za su dauka a kan wacce ake zargi da safarar matan, shugaban hukumar ya ce za su gurfanar da matar a gaban kotu don hukunta ta bisa laifin da ake zargin ta aikata, wanda ya saba da sashe na 70 a Kundin Manyan Laifuffuka na hukumar wanda aka yi masa gyaran fuska a shekarar 2015.