✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai tabin hankali ne ya yi harbin kai mai uwa da wabi a Amurka – Jami’ai da ’Yan uwa

Jami’an tabbatar da doka a Amurka sun bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AP cewa m’aikacin kwantiragi a rundunar sojan ruwan Amurka, wanda ya yi…

Alexis Aaron, wanda ya yi harbin  kan-mai-uwa-da-wabiJami’an tabbatar da doka a Amurka sun bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AP cewa m’aikacin kwantiragi a rundunar sojan ruwan Amurka, wanda ya yi harbin kan-mai-uwa-da-wabi, Aledis Aaron, ya yi fama da tabin hankali, har da matsalar rashin barci. Yana jin sakonni ta ko’ina a cikin kansa, inda yake jin muryoyi daban-daban.
Wannan ma’aikacin kwantiragi ya yi amfani da katin izin aikinsa, wajen shiga kebabben wuri a cikin ofishin rundunar sojan ruwan Amurka, inda ya hau saman wasu na’urori ya yi ta harbe-harbe, har sai da ya halaka mutum 12, inda daga bisani shi ma aka kashe shi.
Aaron Aledis, dan shekara 34, an yi masa magani a wajen kula da lafiyar tsofaffin sojoji, kamar yadda jami’an hukuma suka bayyana. Majiyar da ta bayar da bayani a kansa, ta ce ba ta so a ambaci sunanta, domin har yanzu ana gudanar da bincike kan musababbin abin da ya sanya ya yi harbin kan mai uwa da wabi. Rundunar sojan ruwa ba ta taba ayyana shi a matsayin mahaukaci ko mai tabin hankali da ba zai iya gudanar da aikinsa ba, da tuni an hana shi izinin gudanar da aikinsa na jami’in tsaro.
Iyayensa da ’yan uwa sun bayyana wa masu bincike cewa Aledis yana karbar maganin tabin hankali.
Masu bincike sun kasa gano hakikanin dalilin da ya sanya ya yi wannan harbi mai ban mamaki, wanda ba a taba ganin irinsa ba, tun bayan kisan gillar da aka yi a Fort Hood da ke Tedas, a shekarar 2009. Sai dai masu binciken sun gano cewa shi wanda ake zargi da yin harbin kan mai uwa da wabi, tamkar mabiyin addinin Buddha ne; kuma yana fama da kadaici; yana da saurin harzuka. Sannan ya yi korafi kan yadda aka nuna masa wariya a rundunar sojan ruwan, har da  takaddamar da ya sha yi da jami’an tabbatar da doka, a wani yanayin ma har da harbe-harbe a sakaninsu. Marigayin dan bindigar ya sha sasanta rikicin a dakin ibadar addinin Buddha, har ma ya koya wa kansa yaren mutanen Thailand.
Aledis ya yi amfani da makaman da suka hada da bindiga samfurin AR-15 da gajeriyar bindiga da wata karamar bindiga da ya kwace a hannun wani dan sanda, a lokacin da yake harbin, kamar yadda wata majiya ta jami’an tabbatar da doka ta bayyana wa manema labarai. Nau’in bindigar da ya yi amfani da ita, irinta aka yi amfani da ita wajen kisan gillar da aka yi wa kananan yara ’yan elemantare a garin Newtown, inda dalibai 20 suka rasa rayukansu, tare da mata shida. Irin wannan bindiga an yi amfani da ita a wajen kallon wasannin kwaikwayo da fina-finai na Colorado, inda aka halaka mutum 12 aka kuma jikkata mutum 70.