✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta dakatar da tantance kwamishinoni a Jihar Katsina

Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta dakatar da tantance mutanen da Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya tura mata domin ba su mukaman kwamishinoni. Sunayen mutum…

Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta dakatar da tantance mutanen da Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya tura mata domin ba su mukaman kwamishinoni. Sunayen mutum 17 ne, Gwamnan ya tura ga majalisar don tantancewa wadanda shida daga cikin sun taba rike wannan mukami a zangon farko,

Wannan mataki da ’yan majalisar suka dauka ya zamo irinsa na farko a tarihin jihar, domin abin da aka saba shi ne da zarar Gwamna ya tura sunayen wadanda yake son ba mukamin kwamishinonin, nan da nan majalisar za ta tantance su ba tare da bata lokaci ba, sai kuma Gwamna  ya nada su tare da ba kowa ofishin da zai yi aiki.

To amma a wannan karo an samu akasin haka bayan mika wadannan sunaye kuma aka kira su a majalisar don tantancewa yadda aka saba. amma bayan wani zama da majalisar ta yi, sai aka dage zaman majalisar har sai abin da hali ya yi.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin wasu ’yan majalisar kan dalilinsu na daukar wannan mataki, amma yunkurin ya ci tura, Sai dai kuma kamar yadda wadansu daga cikin jama’ar gari da Aminiya ta nemi jin ta bakinsu, wadanda suka ki yarda a ambaci sunayensu, suka c, akwai zargi ko korafin cewa, mafi yawan wadanda ake son ba mukaman yaran wani mutum ne mai karfin fadi-a-ji a jihar. Duk da kin ambata sunan wanda ake zargin da tura mafi yawa daga cikin sunayen kamar yadda aka yi a zangon farko na mulkin, amma an ce masu adawa da haka ne suka nuna kin yarda.

Sannan akwai masu cewa kin biyan wasu bukatun ’yan majalisar na da nasaba da wannan mataki na majalisar ta dauka. Masu wannan ra’ayi na cewa, tun farkon kawo sunayen, sun ji wani dan majalisar na nuna korafi a fili dangane da aikin tantancewar.

Dan majalisar ya yi korafin cewa, ko shi kansa akwai wasu bukatu da ya tura wa Gwamnan na jama’arsa, amma babu wani abin da aka yi har zuwa wannan rana.

Wadansu kuma na cewa, shigo da wadansu mutanen da ba su dade da dawowa cikin Jam’iyyarAPC mai mulki ba na da nasaba da wannan lamari. Masu wannan ra’ayin na cewa, babu yadda za a yi ga wadanda aka sha wuyar jam’iyya da su har aka kafa gwamnati amma a ce ana barinsu a baya a wajen bayar da wadancan mukamai.

Ha ’ila yau, wani sashen masu ra’ayin na ganin cewa, wadansu ne ke ganin muddin suka bari aka nada wadannan mutane da Gwamna Masari ya kai, to lallai babu makawa an bata musu duk wani yunkuri da manufa ko kudirin da suke da shi a zaben shekarar 2023, saboda suna da wata rawar da suke son takawa in lokacin ya zo. Har zuwa rubata wannan rahoto, babu wani martanin da ya fito daga bangaren Gwamna Masari wanda ya dawo jihar a ranar Litinin da wannan lamari ya faru bayan zuwansa aikin Umara tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari