Search
Subscribe
Majalisar Dinkin Duniya ta zabi Dangote da Adesina don jagorantar yaki da rashin abinci mai gina jiki

Daga hagu Aliko Dangote da Akinwunmi Adesina

Majalisar Dinkin Duniya ta zabi Dangote da Adesina don jagorantar yaki da rashin abinci mai gina jiki

Majalisar Dinkin Duniya ta nada Alhaji Aliko Dangote Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote da Mista Akinwunmi Adesina Shugaban Bankin Raya Afirka su kasance cikin shugabanni 27 da za su yi yaki da rashin abinci mai gina jiki a duniya.

Nadin ya samu sahalewar Babban Sakataren Majalisar Mista Antonio Guterres, inda za su yi aiki tare da kungiyar fadada samar da abinci mai gina jiki (Scaling Up Nutrition – SUN).

Wata takarda da Kungiyar  SUN ta fitar, ta ce shugabannin  sun hadu ranar Talatar da ta gabata, domin daukar matakan da kungiyar tasa a gaba wato kashi na uku da ake sa ran fara aiwatar da shi  a shekarar 2021 zuwa 2025.

Haka zalika shugabnnin za su sake haduwa domin tsara nasarorin da kungiyar take son cimmawa a taron da za su gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan a badi.

A cikin kowane mutum uku dai  akan samu daya da ke fuskantar karancin abinci mai gina jiki, kuma sama da yara  miliyan 149 suna fama da wannan matsala, wadda take ci gaba kuma ya kamata a duba lamarin don a magance shi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin