Da Dumi Dumi

Majalisar Dinkin Duniya za ta karfafa zaman lafiya a Afghanistan

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya cimma matsaya ta bai-daya, kan a tsawaita tare da karfafa aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Afghanistan, matakin da ya kauce wa barazanar China ta hawa kujerar-na-ki.

A farkon makon nan ne ya kamata kwamitin ya kada kuri’a kan wannan batu, kwana guda kafin wa’adin aikin majalisar ya kawo karshe a kasar.

Sai dai China ta yi barazanar hawa-kujerar-na-ki kan kudirin sabunta ayyukan majalisar a kasar ta Afghanistan, saboda bai hada har da wani shirin ayyukan da ta kirkiro ba, na “samar da ababen more rayuwa kamar samar da hanyoyin kasa da na ruwa, wadanda za su hada Chinanda nahiyoyin Asiya, Turai da Afirka ba.”

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka kai hari a taron yakin neman zabe a Afghanistan. Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya tsallake rijiya da baya yayin wani harin kunar bakin wake da ya hallaka kimanin mutum 30, harin da ’yan Taliban suka dauki alhaki kaiwa.

Wani harin kunar bakin wake da ’yan Taliban suka kai ya hallaka akalla mutum 30 a Afghanistan ranar Talata, hari mafi muni da aka kai kusa da wani wurin gangami da Shugaba Ashraf Ghani ya halarta. Sai dai shugaban ya tsallake ba tare da ko kwarzane ba.

ADVERTISEMENT

Harin dai ya zo kwana 11 gabanin zaben Shugaban Kasa a Afghanistan wanda kwamandojin Taliban suka yi alwashin sai sun wargaza  kuma a daidai lokacin da ake tattaunawar zaman lafiya tsakanin kungiyar Taliban da kuma Amurka.

Shugaba Ashraf Ghani wanda ke neman wa’adi na biyu na shekara biyar a zaben da za a yi a ranar 28 ga watan  nan na Satumba yana shirin gabatar da jawabi a taron gangamin lokacin da dan kunar bakin waken ya kai harin.

Share