✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dokokin Zamfara ta nemi a sauke Shugaban Hukumar UBE

MajalisarDokokin Jihar Zamfara a karkashin jagorancin Alhaji Sanusi Garba Rikiji ta nemi a kori Shugaban Hukumar Ilimi Ba-daya (UBE) ta Jihar Alhaji Murtala Adamu Jangebe…

MajalisarDokokin Jihar Zamfara a karkashin jagorancin Alhaji Sanusi Garba Rikiji ta nemi a kori Shugaban Hukumar Ilimi Ba-daya (UBE) ta Jihar Alhaji Murtala Adamu Jangebe sakamakon zarginsa da wani kwamitin da majalisar da almubazzaranci da kudin hukumar har Naira biliyan daya da miliyan 61 da dubu 871 da 975 da kwabo 54.
Majalisar ta bayyana haka ne a cikin wata takarda dauke da sanya hannun Mukaddashin Akawun Majalisar Isa Abdullahi Bayero ya sanya wa hannu a kai, inda ta bukaci shugaban Hukumar UBE din ya amayo wadannan kudade ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.
Majalisar ta kuma nemi a a haramta wa shugaban rike kowane irin mukamin gwamnati, inda wakilan majalisar suka yi ittafkin ba su amince da shugabancinsa ba, inda suka ba da umarnin kada ya sake amsa sunan shugaban wannan hukuma ta UBE.
Sun kara da cewa sun amince kan cewar dukkan masu hannu a cikin laifuffukan zargin karkatar da kudi, a ladabtar da su, a karkarshin ofishin Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar.
’Yan Majalisar sun yarda cewa dukkan kudin da aka gano dole a maida su ta fannin daukar malaman da suka kammala digiri a fannin koyarwa a Jihar Zamfara, bugu da kari sun yarda cewa a yi amfani da kudaden wajen daukar malaman makaranta kamar yadda gwamnati ta yi alkawarin daukarsu.
An zargi Jangebe da almubazzaranci da Naira miliyan 745 ne kafin kudi ya haura zuwa samada Naira biliyan daya.
Jangebe ya taba zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.
Duk kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakinShugaban na UBE a Jihar Zamfara Alhaji Murtala Adamu Jangebe kan wannan matsayi ya ci tura, saboda wayarsa ba ta shiga, kuma lokacin da wakilinmu ya je gidansa an ce baya nan.