✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Al’irshadiyya ta yaye dalibai matan aure karo na farko cikin shekaru 12 a Legas

A karshen makon jiya ne Makarantar Al’irshadiyya ta yi walimar yaye dalibai matan aure tara da suka sauke Alkur’ani Mai girma a Unguwar Mil 12…

A karshen makon jiya ne Makarantar Al’irshadiyya ta yi walimar yaye dalibai matan aure tara da suka sauke Alkur’ani Mai girma a Unguwar Mil 12 da ke Legas a karon farko cikin shekaru 12 da kafuwarta inda aka bai wa daliban shaidar kammala karatu.

Malama Maryam Dayyabu ita ce shugabar makarantar ta shaida wa Aminiya cewa makarantar ita ce irinta ta farko a yankin, wadda take da malamai mata zalla masu koyar matan aure. Ta ce ta kafa makarantar ce da dalibai biyar zuwa bakwai inda ta sha gwagwarmaya kafin ta kai ga cimma manufarta na bai wa iyaye mata ilimi.  “Na yi gwagwarmaya kwarai kafin in kai ga kafa wannan makaranta. Na jajurce ne lura da muhimmancin ilimin mata tare da rauninsu da sakacinsu ta fuskar neman ilimi, wadannan dalilai ne suka sanya na dage har Allah Ya taimake mu muka kai ga kafa wannan makaranta wacce a yanzu muke yi a wani gida a Unguwar Mil 12 a Legas. Fatarmu ita ce mu kai ga mallakar ginin makarantarmu domin kyautata ayyukan koyo da koyarwa da muke yi wanda hakan ne zai ba mu damar fadada makarantar daga dalibai 80 da muke da su a halin yanzu,” inji ta.

Shugabar ta ce duk da cewa  akwai makarantun matan aure da dama a yankin, amma maza ne ke koyar da matan auren kuma ba duk namiji ba ne ke lamuntar malami namiji ya koyar da iyalinsa, “Dama  ciwon ’ya mace na ’yar uwarta  mace ne, idan mace ce take koyar da mata za su fi samun daidaito domin za a samu ikon fayyace komai ba tare da matsalar jin kunya ko wani abu makamancin haka ba. Daliban za su samu kwarin gwiwar tambayar duk wani abu da ya shige musu duhu, malama mace za ta samu sukunin amsa musu tambayoyinsu yadda ya kamata, wannan kadan ne daga cikin dalilan da muka ba da himma domin cimma manufofinmu,” inji ta.

Malama Maryam ta ce dalibai matan da aka yaye an ba su shaidar kammala zangon karatunsu, kana za su ci gaba da tallafa mata wajen koyar da matan aure da ’yan mata da zawarawa. Ta ce idan burinsu na mallakar ginin makarantar ya cika za su fadada ta domin amfanin al’ummar yankin.

Daya daga cikin daliban da suka yi saukar, Hajiya Hadiza Abubakar ta shaida wa Aminiya cewa za su yi amfani da abin da suka koya wajen kyautata tarbiyyar ’ya’yansu tare da karatunsu, kuma ta sha alwashin ba da gudunmawar domin ci gaban makarantar.

Ta yi kira ga ’yan uwanta mata su ba da himma wajen neman ilimi domin shi ne gishirin rayuwar duniya. A karshe ta gode wa mazansu da suke ba su kwarin gwiwa wajen neman ilimi.

Alhaji Abubakar Faki, Garkuwar Faki daya daga cikin iyayen makarantar ya yi kira ga maza su tabbatar sun sauke nauyin matansu na ba su ilimi. Ya ce a baya akwai masu kyamar namiji ya koyar da matansu, amma yanzu an ci gaba ta yadda ake samun mata hazikai masu koyar da ’yan uwansu matan aure, don haka kamata ya yi a yi amfani da wannan dama domin  bunkasa ilimin iyaye mata, “Akasari za ka ga namiji ya dawo daga kasuwa ko aiki ko sana’a a gajiye cikin kurarren lokaci ka ga ba ya da damar ya koya wa iyalinsa karatu, amma tunda sauki ya samu ana samun malamai mata na koyar da ’yan uwansu, to kamata yayi mu ba da himma mu mara musu baya domin amfanin kanmu tare da sauke nauyin da Allah Ya dora mana,” inji shi.