✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Hidayatul Muslimin ta Akim Kalaba ta yaye dalibanta

Makarantar Islamiyya ta Hidayatul Muslimin da ke barikin sojan ruwa na Akim Kalaba a Jihar Kuros Riba ta yi bikin yaye dalibanta, goma sha daya…

Makarantar Islamiyya ta Hidayatul Muslimin da ke barikin sojan ruwa na Akim Kalaba a Jihar Kuros Riba ta yi bikin yaye dalibanta, goma sha daya da suka kunshi maza biyar da mata shida.
Sakataren kungiyar  iyaye da malaman makarantar, Malam Musa Muhammad Kutama ya bayyana cewa shugaban kungiyar Iyaye da Malaman makarantar, Alhaji Haruna Ibrahim shi ne ya raba wa daliban takardar shaida da kuma wasu kyautuka yayin walimar yaye daliban.
Ya ci gaba da cewa makarantar ta bullo da shirin karatu mataki na sakandare, wanda tuni ma aka yi yunkurin farawa da daliban da aka yaye, wanda tuni babban limamin barikin, Laftana-Kwamanda M. B. Zakariyya ya ce da an bude makarantar, za a fara karantarwa a wannan zangon karatu.
Sai dai ya jawo hankali kan wasu kalubale da makarantar Islamiyyar ke fuskanta da suka hada da karancin wurin zagayawa da bukatar rijiyar burtsatse da lantarki . “Akwai bukatar iyaye da kuma sauran masu kwadayin lada su bayar da gudunmawa domin a magance matsalolin”. Inji shi.
Malaman da suka yi jawabi yayin walimar sun jawo hankalin iyayen yara wajen nauyin karantar da iyalansu da Allah Ya wajabta musu tare da baiwa ’ya’ya tarbiyya tagari.
Kana kuma an kara tunatar da jama’ar musulmi kan  muhimmancin amana da kuma rike ta.