✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Misbahul Islam Manchok ta yi saukar karatu

Makarantar Islamiyya ta Misbahul Islam da ke garin Manchok a Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna ta yi saukar karatun Kur’ani Mai girma karo na…

Makarantar Islamiyya ta Misbahul Islam da ke garin Manchok a Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna ta yi saukar karatun Kur’ani Mai girma karo na 12, inda aka saukar da maza takwas da mata hudu.

Da yake gabatar da nasiha ga daliban bayan jagorantar darasun da ya yi, Sheikh Aminu Kassim Kafanchan ya yi kira ga matasa da su rungumi ayyukan ibada da yin watsi da sharholiya da ya dauke wa matasa hankalin a wannan zamani.

Sannan ya yi kira ga daliban da suka yi saukar da su jibinci Alkur’ani ya zama samfurin rayuwarsu kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya gudanar da rayuwarsa ta yadda ba za ka iya raba shi da Alkur’ani ba. Sannnan ya janyo hankalin jama’a kan muhimmancin koyo da karantar da karatun Alkur’ani Mai girma.

A karshe ya yi kira ga daliban da suka yi saukar da su sani yanzu suka fara neman ilimi.

Da yake yi wa Aminiya karin haske, daya daga cikin shugabannin makarantar, Alkali Adamu Danjuma ya ce makarantar wacce shi ma ya yi dalibta a ciki ta shekara wajen 80 da kafawa.

Alkali Danjuma ya ce ba zai iya tantance yawan daliban da makarantar ta yaye tun tana makarantar allo har zuwa rikidewarta zuwa makarantar Islamiyya ba, sannan ya bayyana farin cikinsa da damar da Allah Ya ba su ta ci gaba da rike makarantar da suka gada iyaye da kakanni.

A karshe ya yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wa makarantar don yin gini da kuma mayar da ita ta zamani domin a cewarsa, babu isassun ajujuwa a makarantar lura da irin muhimmancin da makarantar ke da shi a yankin da kuma karuwar ’ya’ya da jikoki don kada makarantar ta kasa a nan gaba.