✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Sa’adatul Abadiyya ta yaye mahaddata  37

Makarantar Koyar da Karatun Alkur’ani Mai girma ta Sa’adatul Abadiyya da ke Jos da fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Abubakar Bafulatani ya assasa ta yi…

Makarantar Koyar da Karatun Alkur’ani Mai girma ta Sa’adatul Abadiyya da ke Jos da fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Abubakar Bafulatani ya assasa ta yi bikin yaye dalibanta 37 da suka haddace Alkur’ani Mai girma da dalibai 51 da suka sauke littafin Diwani.

Da yake jawabi a wajen yaye daliban, Sheikh Abubakar Bafulatani, ya ce an bude makarantar ce shekara 50 da suka gabata.

Ya ce kafin a samu rikice-rikicen da aka yi a baya a Jihar Filato, daliban makarantar sun kai sama da 500. Amma yanzu daliban ba su wuce 200 ba.

Sheikh Bafulantai ya ce a makarantar ana koyar da karatun Alkur’ani Mai girma da littafin Diwani da sauran littattafan addinin Musulunci da karatun boko.

“Muna ciyar da dalibanmu da safe da rana da daddare. Kuma muna daukar nauyin ciyar da su. Kuma idan rashin lafiya ya kama su, mu muke daukar nauyin magani, ba sai mun tura wa iyayensu ba. Kuma muna ba su wuraren kwanciya,” inji shi.

Ya ce saboda su taimaka wa addinin Musulunci ya sa ba sa barin dalibansu su yi bara. “Domin a yanzu yin barace-barace abin kunya ne a Najeriya,” inji shi.

Sheikh Bafulatani ya kara da cewa ya kamata duk malamin da zai karantar da yara ya san yadda zai yi ya rika daukar nauyin almajiransa, su rika zama suna karatu ba tare da sun hada da bara ba. A karshe ya yi kira ga iyaye da gwamnati su taimaka wa  makarantar.

A jawabin daya daga cikin malaman makarantar Sayyada A’ishatu Sheikh Abubakar Alfallati da aka sani da Sayyada Alaika, ta ce babban burinsu kan makarantar shi ne su samar mata da mazauni na musamman da za su kara bude sababbin ajujuwa.

Ta yi kira ga jama’a su tallafa a samu filin da za a gina mazaunin makarantar.