✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Ummu Aiman ta yi bikin saukar dalibanta

Makarantar Matan Aure ta Ummul Aiman da ke Unguwar Yalwa a Karamar Hukumar Dala a Jihar Kano ta yi bikin saukar Alkur’ani Mai girma da…

Makarantar Matan Aure ta Ummul Aiman da ke Unguwar Yalwa a Karamar Hukumar Dala a Jihar Kano ta yi bikin saukar Alkur’ani Mai girma da dalibanta suka yi a ranar Lahadin da ta gabata.

Aminiya ta gano cewa dalibai 19 ne suka sauke Alkur’ani Mai girma a karo na biyu a makarantar inda ta  gudanar da makamancin wannan taro a shekarar 2014.

A jawabin Shugabar Makarantar Sayyada Ummu Aimana Sadik Sallau ta bayyana farin cikinta da ganin wannan rana tare da tabo kadan daga tarihin makaranatar inda ta ce an kafa ta ce shekara 18 da suka gabata da dalibai 15, inda a yanzu makarantar ke da dalibai 60.

Sayyada Ummu Aimana ta ce bude makarantar da ta yi yana daga cikin burin mahaifinta wanda ya yi ta kokari don ganin ta ilimantu kwarai yadda za ta gaje shi kasancewarsa na mai bayar da ilimi kafin rasuwarsa.

Bako mai jawabi Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana muhimmancin ilimin mata inda ya ce idan aka samu mata suka yi ilimi za a sa mu kyakkayawar al’umma lura da cewa iyaye mata su ne jigon tarbiyya yara.

A jawabin Malam Rufa’i Uba Gabari wanda kuma shi ne malami mai darasu nuni ya yi game da falalar Alkur’ani inda ya ce masu karanta Alkur’ani ba su kadai ke fa’idantuwa da albarkarsa ba har da ’ya’yansu.

Ya bayyana muhimmancin koyo tare da koyar da Alkur’ani Mai girma inda ya kafa hujja da Hadisin Manzon Allah (SAW) da yake bayyana cewa mafi alherin mutane shi ne wanda ya koyi Alkur’ani sannan ya koyar da shi ga wadansu.

Da yake ta’aliki a wajen taron Shaikh Dokta Aminu Sagagi kira ya yi da a kara bude makarantun matan aure a ko’ina tare da samun hazikan mata su samu ilimi da za su rika koyar da ’yan uwansu mata.

Sannan ya yi kira ga daliban da suka yi saukar su jajirce wajen ci gaba da bibiyar karatunsu ba wai kawai su ajiye karatun gaba daya ba.