✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makiyaya na bukatar a yi musu adalci- Miyetti Allah

kungiyar Fulani makiyaya na kasa reshen Jihar Bauchi ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatocin Jihohi da su yi wa Fulani Makiyaya adalci…

kungiyar Fulani makiyaya na kasa reshen Jihar Bauchi ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatocin Jihohi da su yi wa Fulani Makiyaya adalci domin bunkasar tattalin arziki da samun dawwamammiyar zaman Lafiya da ci gaban kasar nan. 

Sakataren kungiyar na Jihar Bauchi, Alhaji Sadik Ibrahim Boto ne ya yi wannan kira a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, ya ce “Rashin adalci da Fulani ke samu daga dukkan hukumomin Gwamnati shi ne babban dalilin da yasa aka raina fulanin kuma akowane lokaci ake mai da su baya tamkar ba ‘yan kasa ba.

Ya ce a kasar nan duk da cewa Fulani na bada kaso mai tsoka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa kamar samar da Nono da Madara, da fatu da kirgi da kuma biyan haraji, makiyaya ne kawai suke rasa kaso cikin kasafin kudi na tarayya, jihohi da kananan hukumomi.

Sakataren ya ce “Da zaka ji cewa an tanada a ma’aikatar gona, a karshe zaka ga manoma ne ake baiwa ba wani abu na makiyayi alhali su manoman kuma a karshe sune za a je a hada su fada da makiyayan, kuma in ka dubi tarihi, dukkan manyan hanyoyin kasar nan an gina su ne akan labin shanu, amma ba wadansu sabbin hanyoyin shanu da aka sake fitarwa wa Fulani, don haka mutum ne ka tare masa hanya ka tare masa wajen shan ruwa kuma ka ce ya zauna a waje guda, ta ina zai zauna? dole sai gwamnatoci sun yi musu adalci kafin su zauna waje guda”.

Sai ya godewa Gwamnatin Jihar Jigawa saboda yadda ta gina sabbin labi da burtalin shanu sannan ya roki sauran Gwamnatoci da su yi koyi da haka domin samun zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.