Makiyayi ya sare kan budurwar sa dan taki ba shi hadin kai

Wani matashin bafulatani makiyayi da ke zaune a Ilasa a jihar Ekiti ya sare kan kan budurwar sa, ta mutu a ranar Talatar da ta gabata a lokacin da budurwar wacce ita ma bafulatana ce ta je rafi dibar ruwa tare da kanwar ta, inda ya sunbace ta a daidai lokacin da ta tsuguna ta na dibar ruwa, saboda rashin ba shi hadin kai, sai ya yi kanta ya cakumota ya sare da adda ya cire mata kai.

Majiyar mu ta shaida cewa, matashin ya gudu biyo bayan aika-aikar da ya yi amma bisa bayanan da ‘yar uwan marigayiyar tayi aka yi nasarar kama shi.

Marigayiyar ta fara juyawa saurayin nata baya ne biyo bayan halayansa na shaye-shaye da ya tsunduma a ciki lamarin da ya fusa ta shi ya hallaka ta.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti Caleb Ikechukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, rundunar na kan binciken lamarin.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya