✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malamin makarantar kauye ya samu kyautar Naira miliyan 360

Masu iya magana sun ce alheri danko ne ba ya faduwa kasa banza. haka ne ya faru da wani malamin makaranta a wani kauyen kasar…

Masu iya magana sun ce alheri danko ne ba ya faduwa kasa banza. haka ne ya faru da wani malamin makaranta a wani kauyen kasar Kenya mai suna Peter Tabichi wanda ya saba bayar da akasarin albashinsa domin taimaka wa dalibai marasa galihu a karshe ya lashe kyautar gwarzon malami na duniya. Peter Tabichi ya samu Dala miliyan 1, (kimanin Naira miliyan 360) kan wannan aiki nasa.

Malamin ya samu yabo kan taimaka wa wata makaranta mai karancin ajujuwa da yawan dalibai.

Mista Peter wanda yake koyar da darasin kimiyya ya ce yana so dalibai su nakalci kimiyya domin kawo ci gaba a rayuwar gobe.

An bayyana malamin wanda aka ba shi kyautar a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a matsayin wanda ya yi fice wajen taimaka wa dalibai da suke a karkara a kasar Kenya.

Malamin na bayar da kashi 80 cikin 100 na albashinsa ne ga dalibansa.

Habbaka kimiyya

Daliban da Mista Peter yake taimaka mawa akasarinsu marayu ne ko kuma sun fito daga gidajen marasa galihu.

Malamin ya ce yana so ne ya kara cusa soyayyar darasin kimiyya da kuma kara kawo ci gaba a fannin kimiyya ba wai a kasar Kenya kawai ba, har a Nahiyar Afirka.

Bayan ya lashe kyautar, malamin ya yaba da kwazon matasan Afirka kamar yadda BBC ya ruwaito.

Ya ce, “A matsayina na malamin kimiyya da nake tare da dalibai kullum, ina ganin yara masu kwazo da fasaha da kuma baiwa iri-iri. Ina sa ran cewa Afirka za ta samar da masana kimiyya da injiniyoyi da manyan ’yan kasuwa wadanda za a san da su a duniya, kuma yara mata za su kasance a cikinsu.”

Aikin koyarwa

Mista Peter ya ce irin kalubalen da yake fuskanta a matsayin malami shi ne irin kokarin da yake yi domin wayar da kan mutanen karkara kan muhimmancin ilimi da kuma kai ziyara ga iyayen yaran da akwai barazanar yiwuwar cire su daga makaranta.

Mista Peter yana kokarin sauya ra’ayin iyayen da suke kokarin aurar da ’ya’yansu da wuri inda yake ba su shawarar su bar ’ya’yansu mata su yi karatu.

Mista Peter ya ce wannan kyautar da ya samu ta nuna cewa yana kan hanya madaidaiciya.

Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya taya malamin murna kan kyautar da ya samu.

Ana bayar da wannan kyauta ce duk shekara domin kara darajar aikin malanta.