✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mali: Sojoji sun dage taron kafa gwamnatin farar hula

Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali sun dage taron farko da suka kira kan mika ragamar kasar ga hannun gwamnatin riko ta…

Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali sun dage taron farko da suka kira kan mika ragamar kasar ga hannun gwamnatin riko ta farar hula.

Ana dab da fara taron da suka shirya ne suka sanar da dage shi saboda abun da suka kira ‘dalilan aiki’ a zaman da aka gayyato kungiyoyin kare hakki da na siyasa da tsoffin ’yan tawaye.

Korafin gamayyar kungiyoyin da suka jagoranci zanga-zangar da ta kai ga yi wa Shugaba Ibrahim Boubacar Keita juyin mulki, ya sa sojojin dage taron na ranar Asabar, zuwa lokacin da ba su bayyana ba.

Rashin gayyatar kungiyoyin ya jawo zargi sojojin da neman yin mamaya a hambarar da gwamantin da ta shude.

Kungiyoyin da suka jagoranci zanga-zangar da aka fara a ranar 5 ga watan Yuni, sun nemi a ba su dama a gwamnatin rikon kwaryar saboda rawar da suka taka wajen ganin baya gwamantin Shugaba Keita a ranar 18 ga Agusta.

Sojojin sun yi alkawarin gayyatar kungiyoyin zuwa zaman da za a yi, duk da cewa sojojin ba su fitar da jadawalin zaman nag aba ba.

“Muna takaici cewa sojojin da suka sa jama’a na yin kyakkyawan fata…na neman karkacewa daga mutane”, inji Tahirou Bah na kungiyar Espoir Malikoura, daya daga cikin wadanda suka jagoranci zanga-zangar Mali.

Daga baya kungiyoyin sun ce sojojin sun gayyace zuwa barikin Kati, mai makwabtaka da birnin Bamako a ranar Asabar, domin ganawa da shugabannin juyin mulkin.

Ana iya tunawa bayan shafe makonni zanga-zangar masu adawa na karuwa a Mali ne wasu fusatattun kananan hafsoshin soji suka hambarar da gwamnatin Shugaba Keita da Firaiminista Boubou Cisse, wadanda suke ci gaba da tsarewa tare da wasu shugabannin kasar.

Juyin mulkin da sojojin suka yi ya sha kakkausan suka daga kasashen duniya da tuni suka fara yanke hulda da Mali ta hanyar da dakatar da ita daga harkokinsu da janye tallafin da suke ba ta.

Tuni dai kasashe musamman na Yammacin Afirka suka ba da wa’adin wata 12 ga sojojin su mika ragamar jagorancin kasar a hannun gwamnatin riko ta farar hula sannan su saki dukkannin shugabannin da suka tsare ba tare da wani sharadi ba.

Kasashen Yammacin Afirka na cikin damuwa game da juyin mulkin kasar wadda ke fama da rikice-rikicen kabilanci da durkushewar tattalin arziki baya ga hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.