✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mali ta yi waje da Najeriya a gasar ’yan kasa da shekara 20 ta Afirka

Ashekaranjiya Laraba ce  kasar Mali ta yi waje da kungiyar kwallaon kafa ta Flying Eagles ta Najeriya a gasar Nahiyar Afirka na ’yan wasan kasa…

Ashekaranjiya Laraba ce  kasar Mali ta yi waje da kungiyar kwallaon kafa ta Flying Eagles ta Najeriya a gasar Nahiyar Afirka na ’yan wasan kasa da shekara 20 a wasan kusa da karshe.

Mali ta doke Najeriya ce a bugun da kai sai mai tsaron gida, inda ta zura kwallo hudu cikin biyar, Najeriya kuma ta zura 3.

A farkon wasan, ’yan wasan Najeriya ne suka fara da abin arziki, wanda hakan ya sa suka fi ’yan wasan kasar Mali taka leda da kusan kashi 63 cikin 100.

’Yan wasan Najeriya, wadanda suke sanye da bakin roba a hannunsu na hagu domin jimanin rasuwar tsohon koci kuma mamba a Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) Taiwo Ogunjobi, sun yi rashin sa’a domin sau biyu suna samun damar zura kwallo suna bararwa. Da farko Alhassan Adamu ya jefa bugun tazara kusa da raga, sannan Yahaya Nazifi ya yi rashin sa’a jim kadan bayan wannan. Mai tsaron gidan Mali, Youssouf Koita shi ne ya cancanci yabo a  wasan, domin ya hana Najeriya zura kwallo musamman a daidai minti 43, inda har an fara murna.

Dan wasan Mali, Mamadou Traore ne ya zura kwallon farko a ragar Flying Eagles ta Najeriya a minti na 78, bayan golan Najeriya Olawale Oremade ya yi sauran bin kwallon. Pascal Onyekashi wanda ya shigo daga baya ne ya farke wa Najeriya inda aka tafi ga bugun finareti..