Search
Subscribe
Mambobin PDP sun yi zanga-zangar kisan shugabar mata ta Kogi

Mambobin PDP sun yi zanga-zangar kisan shugabar mata ta Kogi

A yau Laraba mambobin jam’iyyar PDP mata sun gudanar da zanga-zanga a Abuja akan kisan gillar da wasu matasa suka yi wa shugabar mata ta PDP ta jihar Kogi, Salome Acheju Abuh, wanda ake zargin ‘yan bangar siyasa ne suka banka mata wuta a cikin gidanta.

An dai bankawa Salome wuta ne lokacin kadan da bayyana sakamakon zaben Gwamnan jihar Kogi na ranar 16 ga Nuwamba.

Matan PDP sun fara zanga-zangar ne daga babbar Sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa da ke Abuja zuwa majalisar dokokin kasar, sannan suka wuce ofishin ofishin Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya, don neman masu hakkinsu game da kisan Salome.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin