✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Man United ta xibar wa Inter Milan wa’adin kwana 7 kan Lukaku

Kulob xin Manchester United ya nemi kulob xin Inter Milan da ke Italiya ya gaggauta kammala cinikin Romelu Lukaku nan da kwana 7 muddin yana…

Kulob xin Manchester United ya nemi kulob xin Inter Milan da ke Italiya ya gaggauta kammala cinikin Romelu Lukaku nan da kwana 7 muddin yana bukatar xan kwallon.

Kafar labarai ta UK Mirror da ke Ingila ta ruwaito Manchester United ta sanya farashin Fam miliyan 75 (kimanin Naira biliyan  35 da miliyan 325) ne a kan Lukaku. Sai dai a nata vangaren Inter Milan ta taya xan kwallon ne a kan Fam miliyan 54 (kimanin Naira biliyan 25 da miliyan 434).

Rahotanni sun nuna akwai yiwuwar Mana United ta rage farashin xan kwallon inda hakan zai sa su daidaita.

Kocin Inter Milan kuma tsohon kocin kulob xin Chelsea da ke Ingila Antonio Conte ya zaku ya sayo Lukaku xan asalin Beljiyam daga Man United kafin a fara kakar wasa ta bana.