✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maniyyata sama da milyan 3 daga kasashe 180 zasu yi aikin Haji 2019 

A kalla sama da maniyyata aikin Hajji na shekarar 2019 daga kasashe 180 ake sa ran zasu sauke farali a wannan shekara. Shugaban Kasa Muhammadu…

A kalla sama da maniyyata aikin Hajji na shekarar 2019 daga kasashe 180 ake sa ran zasu sauke farali a wannan shekara.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shaida haka a wajen kaddamar da tashin maniyatan aikin Hajj na wannan shekara wanda aka yi a ranar Larabar nan a filin sauka da tashin jirage na Umaru Musa Ƴar’aduwa da ke Katsina.

Shugaban Kasar wanda ya samu wakilcin Gwamna Masari ya ce, irin wannan haduwar al’umma a lokaci guda saboda aiwatar da wani muhimmin aiki na bautawa Allah ba tare da nuna bambanci sa tufafin alfarma na sarauta ko wani mai kudi ko talakka, samun hakan ba karamin hadin kai bane a tsakanin al’umma. Akan haka Shugaban ya yi kira ga maniyatan da su zamo jakadu na gari a kasa mai tsarki tare da yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya tare da ci gaba.

A nashi jawabin, Shugaban Hukumar alhazai ta Kasa NAHCO Abdullahi Mukhtar Mohammed, ya ja hankakin maniyyatan akan su kiyaye doka da oda tun daga nan gida har zuwa kasar Saudiya. Ya ce, duk maniyyacin da ya karya doka, ba kanshi kawai ya bata ba har da kasa baki daya. Ya kuma ja hankalinsu akan cewa, kada su tafi da duk wani abin da aka ce ba’a shiga da shi acan kasar ta Saudiya musamman Goro da wasu kwayoyin magani da dangin su. Shi dai wannan jirgin farko mai kirar Boeing 747 mai dauke da sunan Marigayi Matawalle Umaru Musa Ƴar’aduwa ya tashi da misalin karfe bakwai da minti 8 na yamma dauke da maniyata 526.