✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma dubu 400 za su shiga noman dawa a bana

A Yayin da manoma ke hankoron samun tan miliyan biyar a bana, ana shirin tallafa wa manoman dawa dubu 400 da nufin yin noman a…

A Yayin da manoma ke hankoron samun tan miliyan biyar a bana, ana shirin tallafa wa manoman dawa dubu 400 da nufin yin noman a damunar bana.

Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban Kungiyar Masu Noma da Sarrafawa tare da Hada-hadar Dawar ta Kasa, NASPPAM, Alhaji Muhammad Babayo Maina da kuma na Sakataren Yada Labarai na Kungiyar, Dakta Sani Hamza, suka fitar a Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewa, kudurin hakan wani bangare ne daga cikin ababuwan da aka cimmawa a karshen taron kaddamar da sabbin sugabannin kungiyar a birnin Abuja. Kamr dai yadda takaddar bayan taron ta nunar, kungiyar ta na hankoron noman Dawar a filayen noma masu fadin kadada Miliyan biyu-da zai samar da kimanin ton Miliyan biyar na Dawar. A cewarsa: “Muna shirin shigar da manoma dubu 400, don noman Dawa, a wannan damunar ta shekarar 2019. Dawa dai ta kasance tamkar ruwan dare gama-duniya, a yankunan arewacin kasar nan; dan haka muke karfafa gwuiwar sauran jihohin kasar, da su taimaka ta fuskar tallafawa manoman Dawar tare da bayar da hekta-hekta na filiyan nomanta.”

Sanarwar ta cigaba da cewa: “Kungiyar na aiki ka’in-da-na’in dan ganin manoman Dawar sun samu damar amfana daga shirin tallafawa manoma na Babban bankin Najeriya, CBN, da ake kira ‘Anchor Borrowers’.

Harwayau, kungiyar ta kuma bayar da umurni ga rassanta na jihohi da kuma kananan hukumomi da su mika bayanan manoman da suka yiwa rajistar shirin, ga babbar Sakatariyar kungiyar ta kasa-kafin nan da 25 ga watan nan.”