✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman albasa sun yi hasarar sama da Naira biliyan daya a Kebbi – Bello Uba

Manoman albasa a Jihar Kebbi sun yi hasarar  albasar sama da Naira biliyan daya, sakamakon wata sabuwar cuta da ba su san kowace iri ce…

Manoman albasa a Jihar Kebbi sun yi hasarar  albasar sama da Naira biliyan daya, sakamakon wata sabuwar cuta da ba su san kowace iri ce ba da ta addabi albasarsu, wadda ta zama dalilin lalacewar albasar.

Shugaban Kungiyar Manoma Albasa ta Jihar Kebbi, Alhaji Bello Uba ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai, a garin Aliero, inda ya ce, akalla manoma dubu 20 ne a halin yanzu matsalar ta shafa a jihar.

Shugaban ya ci gaba da cewa, ’ya’yan kungiyar manoman albasar, sun yi hasarar ce sakamakon bakin cututtukan da ’ya’yan albasar da suka adana a rumbunan ajiyar albasar da kuma irin albasar da suka kamu da bakin cututtuka guda biyu, wadanda kuma ba a san kansu ba.

Ya ce, babbar matsalar ma ita ce manoman ba su da ilimin kimiyyar zamani wanda a cewarsa, zai taimaka musu wajen gano kan cututtukan da yadda za a magance su.

Don haka ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kebbi ta kai musu agajin gaggawa, wajen ganowa tare da tattance irin cututtukan da suka shigo cikin jihar gami da samar da magungunan kashe cututtukan, domin hana ci gaba da aukuwar lamarin.

Daga bisani Matukaddashin Babban Sakataren Ma’aikatar Gona ta Jihar Kebbi, Alhaji Mohammed Lawal, ya ce ma’aikatarsa ba ta da wata masaniya kan dullar wata bakuwar cuta da ta far wa albarkatun gona a jihar. Sai ya shawarci wadanda abin ya shafa, su rubuta takardar kokensu zuwa ga Ma’aikatar Gona ta Jihar Kebbi yana mai bayar da tabbacin cewa, za su duba lamarin kuma za a dauki mataki na musamman domin magance matsalar cikin lokaci.