✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman Citta sun bukaci gwamnati ta shigo ciki

Ganin irin alherin da noman citta ke haifarwa a Kudancin Kaduna, inda aka fi noma shi a fadin Najeriya ya sa Aminiya ta zanta da…

Ganin irin alherin da noman citta ke haifarwa a Kudancin Kaduna, inda aka fi noma shi a fadin Najeriya ya sa Aminiya ta zanta da masu noman citta da ke garuruwa daban-daban da aka fi nomawa don jin irin halin da noman citta ke ciki a wannan shekarar.

kananan hukumomin Kagarko da Jaba da kuma Kachia sune kan gaba wajen noma citta da zabibi a fadin Najeriya yayin da karamar hukumar Jama’a, dukansu dake Kudancin jihar Kaduna, ke biye da su a matsayin na hudu.

Ganin irin alherin da noman citta ke samarwa ta sanya mutane da dama a yankin sun kara rungumar noman citta, wanda a halin yanzu, kasuwarta ke sama tana kasa, ga kuma rashin tsayayyen farashi da ma wasu matsaloli da suka dabaibaye manoma da masu saye, Aminiya ta zanta da wasu daga ciki kamar haka.

Alhaji Sulaiman Jamo Kagarko, wani fitaccen manomin citta ne da ya shafe fiye da shekara 17 yana noman citta wanda ya kewaya da wakilin Aminiya daya daga cikin gonar cittar da ya noma bana, mai tsawon hekta 10 da kuma na zabibi mai tsawon hekta takwas, bayan Aminiya ta ziyarce shi a Kagarko.

“Saboda dagawar darajar citta a kasuwanncin duniya da kuma karuwar masu sayenta ya sanya mutane da yawa da ba su noman citta sun kwararo cikinta sosai a bana. Ni yanzu na shafe fiye da shekara 17 ina noman citta tun ina yi kadan-kadan har ga shi yanzu ina nome hekta 10 na citta da kuma hekta takwas na zabibi,” inji shi.

“Amma babban matsalar da muke fuskanta yanzu abu biyu ne; taki da kuma maganin kwari. Domin abinda ya banbanta noman a da da kuma yanzu shi ne samuwar maganin feshi wanda hakan tasa na kara yawan noman fiye da yadda na ke yi a da. To idan har gwamnati za ta shigo ta rika tallafa mana da maganin nan cikin sauki da kuma taki a kan kari to lallai harkar za ta bunkasa fiye da yadda ake tsammani kuma ba mu kadai manoma ba hatta gwamnatin za ta amfana sosai ta wajen samun kudin shiga.”

Shi ma Alhaji Kabiru Tanko (Ciroman Jama’a) yana daya daga cikin masu noman citta a Kudancin Kaduna. Ga abinda ya ce wa Aminiya yayin da ta tuntube shi kan halin da manoman citta suke ciki a bana.

“Akwai matsaloli da yawa wadanda mu manoman citta ke fuskanta. Na farko ka ga akwai rashin tsayayyen farashi wanda idan ba gwamnati ta shigo ciki ba zai kashewa manoma kwarin gwiwa a kan noman nan. Irin shigowar da muke bukata gwamnati ta yi shi ne na farko ta kafa mana wata hukuma kamar ‘Ginger’s Marketing Board’ wacce za ta rika lura da farashin da za a rika sayen cittan nan ta yadda manoman ba za su rika faduwa ko suna asara ba. Buhun cittan da aka sayar da shi N25, 000 a watannin baya yanzu ana sayar dashi kasa da dubu 10 ne zuwa 8 ake saida shi wanda ka ga haka zai shafi jarin manomi.

“Abu na biyu da mu ke so gwamnati ta taimaka mana da shi shi ne kayan noma na zamani. Har yanzu muna noma ne irin na gargajiya tun daga nomewa da hudewa har zuwa cirewa da yankawa da gyarawa da busarwa duka hanyoyi ne irin na da ake bi wanda baya ga wahalarwa da cin kudi sai ka ga ana samun duwatsu ko kashin dabbobi a ciki. Na ga irin citta na kasashe da yawa da ke noman citta amma ni a wurina kuma ina tsammanin haka abin yake, babu cittan da ya kai namu a duk duniya sai dai rashin tsaftace shi kawai da ba a yi.

“Ya kamata gwamnati ta samar mana da injina da za su rika duk irin wannan aiki da na lissafo da kuma taraktocin noma wadanda hakan zai saukakawa manomanmu kuma zai karawa cittanmu kwarjini a duniya.

“Hanya ta uku da gwamnati ta jiha da ta tarayya za ta iya tallafawa shi ne ta hanyar zuba jarinta a ciki ko gayyatar bankuna don saka hanunsu ko kuma ta sa kananan hukumomin da ake noman cittan (Kagarko da Jaba da Kachia da Jama’a) su zuba hannayen jarinsu a ciki domin bunkasa harkar. Bayan nan ya kamata gwamnati ta samo iri da maganin feshi da kuma taki don tallafawa manoman citta.

“Harkar noman citta na dada bunkasa kuma Masaya na dada tudadowa daga kasashen yankin Asiya da Turai da Amurka da Gabas ta Tsakiya da kasashenmu na Afrika don haka ya kamata gwamnati ta taimaka wajen bunkasa harkar kasantuwar yadda jama’a da dama ke amfana da noman citta.”

Shi ma da yake zantawa da Aminiya, Dangana Habu, wani matashin manomi daga Kurmin Musa a yankin karamar hukumar Kachiya, ya bayyanawa Aminiya cewa shi ya taso ya tarar da iyayensa suna noman citta tun lokacin suna nomawa babu masu saye har zuwa lokacin da ake saye a kan naira dari kowane buhu amma ga shi yanzu kowa ya gane amfaninta har wadanda ba sa noman ta sun fara gwadawa saboda darajarta a kasuwannin duniya.

Dangana, ya bayyana cewa a matsayinsu na manoma suna samun alheri sosai domin zuwa yanzu su ma suna gine-gine suna kuma samun jarin da suke zubawa cikin wasu harkokin kamar sayen motocin haya da Babura da bude shaguna wanda ta hanyar haka suna taimakawa jama’a da dama wajen samar musu da ayyukan yi.

“A yanzu ni ba abin da zan yi da aikin gwamnati domin ina godewa Allah da abinda nake samu a wannan nomar wanda ko wani ma’aikacin gwamnatin bai kaimu samu ba,” inji shi.

“Yanzu duk inda wani ma’aikaci ko mai kudi zai kai ‘ya’yansa karatu a makarantu masu tsada ko da kasar waje ne mu ma zamu iya kai ‘ya’yanmu su yi karatu a wajen, ka ga kuwa a wajena yafi aikin gwamnati.” Ya bayyana.

Dangana, ya bayyana matsalolin da sana’ar noman citta ke ciki, a nasa tunanin, na rashin samar da wata kungiya ta masu noman citta wacce za ta hada kawukansu ko da a matakin karamar hukuma ne wacce kuma zata rika tsaya musu a kowane irin abu ya taso tare da lura musu da farashi.

“Ka ga rashin haka ke sa idan manomi ya shiga cikin wata matsala kuma yana bukatar kudi dole ta sa ya dauko kayansa ya sayar ba a kan kudin da ya kamata ba.” Inji shi

“A matsayin gwamnati wacce ta ke hulda da kasashe kuma wannan sana’ar ya zama na kasa da kasa ka ga gwamnati ce ke da iko kuma ta fi mu ido da masaniyar duk hanyoyin da za a bi don cimma nasara da kuma yadda zata rika shiga tsakani. kasashe da dama da suka hada da Amurka da Chana da Pakistan da Sudan da Saudiyya da Chadi da Jamus da Lebanon da Turkiyya da wasu kasashe da dama duk suna zuwa sayen cittanmu ka ga ya kamata gwamnati ta sa mana hannu.”

Shi ma a karshe ya bayyana cewa babban abinda suke nukata a yanzu shine gwamnati ta taimaka musu da taki da kuma maganin feshi.