✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mansur Isa ne ya zama Zakaran Kokawa na Afirka a bana

Mansur Isah matashin dan kokawa ne mai kimanin shekara 27 wanda yake da nauyin kilog 75.  Kimanin shekara 5 ke nan da fara yin wasan…

Mansur Isah matashin dan kokawa ne mai kimanin shekara 27 wanda yake da nauyin kilog 75.  Kimanin shekara 5 ke nan da fara yin wasan kokawa  amma sai ga shi ya zama Zakaran Kokawa na Afirka na bana a kokawar da aka fafata a kasar Nijar.

Mansur Isah, ya ce a bara ma shi ya lashe gasar kokawar da aka yi a kasar Senegal.

Ya ce duk wadannan gasar kokawa da yake yi, yana wakiltar kasra Nijar ne ba Najeriya ba.

Ya ce nan da wata biyu masu zuwa za a yi wata gasar kokawa ta kasa a babban birnin Tarayya Abuja, kuma Jihar Edo zai wakilta a gasar, don ita ce ta neme shi ya yi haka.  Ma’ana jihar ce ta dauke shi a matsayin aro.

A cewarsa a lokacin da ya fara wasan kokawa babu wanda ya yi tunanin zai tabuka abin kirki sai ga shi duk inda suka je wasa sai ya samu nasara.

Ya ce misali a Nijar akwai wani zakara mai suna Rabi’u Kankura da suka fafata da shi wanda kafin ya kayar da shi sai da suka kwashe kimanin minti 48 suna gumurzu.

Mansur Isah, dai dan asalin Nijar ne amma mazaunin Najeriya.   Ya ce duk da cewa wasan kokawa wasa ne na nishadi idan suna fili ba ya sake fuska saboda kare kambinsa amma idan aka gama wasa yana raha da kowa.

Daga nan sai ya yi kira ga daukacin abokan kokawarsu  su sani kokawa wasa ne ba fada ba don haka kada idan ka fi karfin abokin karawarka, ka kayar da shi yadda za ka yi masa illa.