Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Manyan hare-hare sun firgita Sri Lanka

  • Sababbin bayanai na fito da yadda aka kitsa su

 

Sababbin bayanai suna kara fito da yadda aka kitsa hare-haren da aka kai ga coci a kasar Sri Lanka inda akalla mutum 359 rasu, yayin da kusan 500 suka jikkata.

ADVERTISEMENT

Wakilin BBC da ke Lardin Kolombo ya ce an kara samun wani harin bam a wani otel da ke daura da wani gidan namun daji (Zoo) inda aka kashe ’yan sanda biyu. Sai kuma wani sabon hari da aka kai a Lardin Dematagoda

Wadannan su ne hare-hare na takwas da aka kai a ranar Lahadi a coci-coci da otel-otel a Sri Lanka da suka yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 359.

ADVERTISEMENT

Daga cikin wadanda aka kashe akwai ’yan kasashen waje  35, kamar yadda BBC ya ruwaito.

An dai samu rahotannin tashi bama-bamai shida, kuma coci-coci uku a Kochchikade da Negombo da Batticaloa ne aka kai wa harin a daidai lokacin da ake bukukuwan Ista.

An kuma kai wa otel din Shangri La da na Cinnamon Grand da kuma na Kingsbury hari, kuma dukkan hare-haren sun auku ne a birnin Kolombo.

Sai kuma a yanzu aka kara samun wanda ya zama na bakwai na otel din da ke Lardin Kolombo da na takwas da aka kai a Lardin Dematagoda.

A yanzu haka dai gwamnatin kasar ta saka dokar ta-baci saboda yadda lamarin ke kara ta’azzara.

 

An kama mutum 58

Rahotanni sun ce yanzu haka an kama mutum 58 da ake zargi da kitsa hare-haren.

Ministan Tsaron kasar uwan Wijewardene, ya ce akasarin hare-haren na kunar bakin wake ne, kuma suna zargin kungiya daya ce ta shirya.

Yanzu dai ya bayyana cewa Kungiyar ISI ce ta shirya hare-haren, duk da cewa ba ta kawo dalilin da suka gamsar da cewa ita ta kai harin, wanda hakan ya sa Ministan ya ce ko ma wane ne, za su tabbatar bayan sun kammala bincike.

 

Donald Trump ya jajanta wa mutanen kasar

Shugaban Amurka Donald Trump ya jajanta wa mutanen kasar kan harin. Ya bayyana haka ne a shafinsa na Tiwita inda ya ce kasarsa a shirye take domin ta tallafa.

 

 ‘Masu ilimi ne suka kai harin’

Daya daga cikin maharan ya yi karatu a Birtaniya da Austireliya kamar yadda rahotanni suka nuna.

Ministan Tsaron kasar, Ruwan Wijewardene ya ce, “Daya daga cikin maharan ya yi karatu a Birtaniya, sannan daga baya ya yi karatun sama da digiri a kasar Austireliya kafin ya dawo kasar Sri Lanka da zama.”

Ministan ya ce, “Yawancin maharan sun yi karatu sosai kuma ’ya’yan manya ko masu hannu da shuni ne. Wannan shi ne abin damuwar. Wadansu daga cikinsu suna da digiri biyu a bangarori daban-daban har da masu digiri na biyu a karatun lauya. Don haka ba jahilai ba ne.”

Zuwa shekaranjiya Laraba, Kakakin ’yan sandan kasar uwan Gunasekara ya tabbatar da rasuwar mutum 359,  kuma kusan 500 suke jinya. Sannan an kama mutum 58 ciki har da wanda ya ba daya daga cikin maharan hayar gida.

 

Akwai wadansu maharan a cikinmu – Firayi Ministan Sri Lanka

A jawabin Firayi Ministan Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe ya ce akwai sakaci wajen isar da sako, “Da mun yi abin da ya dace watakila da mun kiyaye aukuwar hare-haren. Shi ma Shugaban Kasa ya fara bincike a kan dalilin da ya sa ban samu labarin cikin sauri ba, domin kuwa an samu labarin cewa kasar tana cikin barazanar tsaro, amma kuma ban sani ba sai bayan aukuwar wannan lamari, kuma ana samun ci gaba a binciken sosai,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Dole a nemo duk wadanda suke da hannu a harin domin wadannan hare-haren ba abin da aka shirya ba ne kawai a nan cikin gida. Abu ne da aka shirya masa sosai.”

Da aka tambaye shi ko yana ganin karshen hare-haren ke nan, sai ya ce, “Har yanzu muna tare da wadansu maharan a cikinmu domin ko a ranar an so a kai wani harin a coci na hudu amma abin ya ci tura,” kamar yadda CCN ta ruwaito.

 

Shugaban Kasar ya bukaci Ministan Tsaro da Shugaban ’Yan Sanda su yi murabus

Shugaban Kasar Sri Lanka, Maithripala Sirisena ya bukaci daya daga cikin ministocin tsaron kasar, Hemasiri Fernando da Sufeto Janar na ’Yan sanda Pujith Jayasundara su yi murabus bisa rashin yin kokarin kare aukuwar lamarin duk da cewa an samu labarin yiwuwar haka.

An samu labarin cewa kasar na fuskantar barazanar harin ta’addanci, wanda hakan ya sa aka fitar da takarda zuwa ofisoshin jami’an tsaron kasar, amma kuma suka ki daukar matakin da ya dace.

 

Muna fuskantar barazana – Musulmin kasar

Wani Musulmi mai suna Mohamed Hasan ya ce tun ranar da aka kai wadannan hare-hare bai sake fita daga gida ba domin tsoron kada a far masa ganin cewa shi Musulmi ne.

Ita ma Zareena Begum mai kimanin shekara 60, ta ce tun ranar da aka kai harin da kyar take samun barci

Mohamed wanda ma’aikaci ne a wani kamfani dab’i ya ce, “Iyalaina sun ce in zauna a gida domin ana iya kashe ni idan na fita.”

Zareena Begum, ta fadi cikin hawaye cewa. “Na san wadansu daga cikinsu suna fushi da Musulmi. Ban taba tunanin irin wannan kiyayyar ba. Amma bai kamata kiyayya ta sake haifar da wata kiyayyar ba.”

 

ISIS ta fitar da hoton wadanda   ta yi ikirari su suka kai harin

A wani rahoto kuma, Kungiyar ISIS ta fitar da hoto da sunayen wadanda ta ce su suka kai harin. A hoton akwai mutum 8, wadanda 7 daga cikinsu fuskarsu a rufe take, daya kuma fuskarsa a bude. Amma kuma hukumomin kasar sun ce ba su tabbatar da sahihancin hoton da kuma ikirarin ISIS din ba.

Kasar Sri Lanka ta ce tana zargin Kungiyar Islamist National Thowheeth Jama’ath (NTJ) ta kasar ce da kitsa harin, sannan kasar ta ce harin bai rasa nasaba da harin da aka kai wa Musulmi a masallaci a New Zealand kwanakin baya ba.

Haka ’yan sanda sun ce suna zargin ’ya’yan wani attajiri mazaunin Kolombo guda biyu da hannu a lamarin, domin sun kasance manya daga cikin mambobin Kungiyar NTJ.

A bayanan ISIS dai, ta nuna cewa Abu Obeidah da Abu Baraa da Abu Moukhtar ne suka kai hari a otel din Shangri-La da Cinnamon Grand da Kingsburry.

Sai Abu Hamza da Abu Khalil da Abu Mohammad suka kai hari a coci uku da ke biranen Kolombo da Negombo da Batticaloa, sai kuma mahari na bakwai da ya kashe ’yan sanda.