✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan mata 10 da badakala ta dabaibaiye kujerunsu

Wasunsu zargin ne ya yi sanadin rabuwarsu, wasu kuma bayan sun sauka ne, wasu kuma har yanzu tsuguno ba ta kare ba.

Yawanci akan siffanta mata da rikon amana fiye da maza, musamma a game da abin da ya danganci sha’anin kudi.

Hakan ya sa hatta a kungiyoyi ake yawan nada mata a mukamin ma’aji da sakataren kudi da sauransu, haka ma a gwamnati.

Amma a baya-bayan nan, zargin badakalar kudi da sauransu ya rika kunno kai a ofisohin wasu fitattun mata da ke rike ko suka rike da manyan mukaman gwamnatin Najeriya.

Wasu daga cikinsu zargin ne ya yi sanadin rabuwarsu da kujerarsu, wasu kuma bayan sun kammala wa’adinsu ne aka fara fuskan bincike.

Ga wasu shahararru daga cikinsu:

1- Sadiya Umar-Farouq:

Zargin karkatar da Naira biliyan 37 ta hannun wan dan kwangila, amma ta musanta sanin dan kwangilar ballantana mu’amala da shi.

2- Betta Edu:

Bakalalar kudaden tallafin masara karfi daga hukumar kula da shirin, da kuma neman amfani da ofishin Akanta-Janar na Kasa wajen karkatar da miliyan 585 na tallafin na jihohi Akwa Ibom, Legas, Kuros Riba da Ogun zuwa asusun wata mata ta.

3- Halima Shehu:

An dakatar da Shugabar Hukumar ba da tallafin dogaro da kai (NSIP), kan tura kudaden gwamnati kimanin biliyan 44 zuwa asusun wasu mutane da hukumomi ba bisa ka’ida ba. Haima dai ta ce ta yi haka ne sakamakon umarni da matsin lamba daga ministar jinkai Bette Edu, amma ita tun da farko ba ta gamsu da hakan ba.

4- Muheeba Dankaka:

Zargin badakalar karbar mili kudade daga hannun masu neman aiki a Hukumar Raba Daidai da kasa da ke karkashin shugabancinta. Muheeba dai ta musanta zargin har ta yi ransuwa a gaban kwamitin majalisar dokoki kasa cewa ba ta da hannu a ciki.

5- Pauline Tallen:

Bayan zargin tsohuwar ministar harkokin mata, Paulin Tallen da karkatar da Naira biliyan biyu, kotu ta haramta mata rike mukamin gwamnati har sai ta janye kalamantan gami da ba ba da hakuri kan saboda ta kira hukuncin Babbar Kotun Jihar Adamawa da ta soke nasarar Aisha Dahiru Binani a zaben da takarar gwamnan jihar na APC a matsain hukuncin je-ka-na-yi-ka.

6- Hadiza Bala Usman:

An zargi tsohuwar Shugaban Hukumar Jiragen ruwa da badakalar biliyoyin kudade da ministan sufuri na lokacin Rotimi Amaechi ke mata, har ta kai an dakatar da ita. Hadizai dai ta a musanta zargin.

7- Kemi Adeosun:

Badakalar amfani da takardar shaidar wa kasa hidima ta bogi, wanda a dalilin haka Kemi Adeosun ta sauka daga kujerarta da ministar kudi a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Kemi ta ce ba ta a san cewa takardar ta bogi ba ce, domin an sama mata ne bisa wakilci.

8- Stella Oduah:

Zargin facaka da kuma karkatar da Naira biliyan biyar sun dabaibaye tsohuwar ministar sufurin jiragen sama a zamanin shugaba Goodluck Jonathan har ya dakatar da ita, zargin da aka jima ana kai-komo tsakanin Stella Oduah da kuma hukumar EFCC. A karshe dai Oduah ta zama Sanata a zamanin magajin Jonathan Muhammadu Buhari.

9- Diezani Alison-Madueke:

Bٍٍadakalar da aka shafe sama da shekaru 10 ana fafatawa da tsohuwar ministar man fetur, wadda ake zargi da wawure biliyoyin kudade. A halin da ake ciki Diezani ta tsere zuwa kasar Birtaniya inda a can ma take fuskantar shari’a.

10- Patricia Etteh:

Shugabar Majalisar Wakilai Dokoki Patrici Ette ta rasa kujerarta a sakamakon badakalar kudaden majalisar da ake zargin ta da facaka da su.