✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maraba da sababbin shugabannin majalisun dokoki na kasa

Zai yi kyau in fara da taya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari murna da a wannan karon ya amince ya kuma dage wajen ganin su wa…

Zai yi kyau in fara da taya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari murna da a wannan karon ya amince ya kuma dage wajen ganin su wa aka zaba shugabannin majalisun dokoki na kasa wato Shugaban Majalisar Dattawa da  Shugaban Majalisar Wakilai da za su ja ragamar majalisar ta 9. Sabanin a shekarar 2015, da aka nemi shugaban ya yi nuni a kan su wa za a zaba su shugabanci majalisun biyu, ya ce “Shi zai iya aiki da duk wanda wakilan majalisun biyu suka zaba shugabanninsu.”

Mai yiwuwa a wancan lokaci Shugaba Buhari yana sabon yankan rake ne a cikin tsarin tafiyar da mulkin dimokuradiyya da tunanin cewa batun tanadin da kundin tsarin mulkin kasar nan ya yi na murhu uku da suke a matsayin shika-shikan mulkin dimokuradiyya kasar nan na kowane bangare ya ci gashin kansa. Wato Bangaren Zartarwa da Bangaren Majalisa mai yin dokoki da kuma Bangaren Shari’a.

Irin yadda Shugaba Buhari tun farko ya ki sa baki a kan su wa za a zaba, ta sanya mutane irin su tsohon Gwamnan Jihar Kwara kuma zababben Sanata a lokacin,  Dokta Abubakar Bukola Saraki da dan Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da a shekarar 2013, suka bar jam’iyyarsu ta PDP, suka koma Jam’iyyar APC, ta su Shugaba Buhari, suka bijire wa umarnin jam’iyyar ta APC, suka shiga takarar mukaman Shugaban Majalisar Dattawa da Shugaban Majalisar Wakilai, suka kuma yi nasara.

Wannan nasara ce, ta sanya cikin tsawon shekara 4 da Jam’iyyar APC ta yi daga shekarar 2015 zuwa 2019, aka yi ta yin kulli-kurciya a tsakanin Bangaren Zartarwa (Shugaban Kasa) da Bangaren Majalisar Dokoki, musamman a Majalisar Dattawa, ta yadda ayyuka suka nemi su tsaya cik a kasar nan., musamman batun amincewa da kasafin kudi na shekara-shekara da batun wasu muhimman nade-naden jami’an gwamnati da dole sai majalisun sun amince da su kana Shugaba Buhari zai iya tabbatar da su.

Mai yiwuwa kokarin kauce wa sake fadawa wancan rudani  na tsawon shekara hudu da irin yadda zuwa yanzu za a iya cewa Shugaba Buhari ya fara koyon yadda ake tafiyar da harkokin dimokuradiyyar kasar nan, ya sanya a wannan karon tun da wuri, ya ce yana goyon bayan Sanata Ahmed Lawan daga Jihar Yobe da Honorabul Femi Gbajabiamila daga Jihar Legas wadanda da ma a 2015, su Jam’iyyar APC, ta mika don su zama Shugaban Majalisar Dattawa da   Majalisar Wakilai, bi-da-bi, lokacin da su Sanata Saraki da Honorabul Dogara suka yi wa APC yankan baya.

A wannan karo ba wai Shugaba Buhari kadai ya dage ba wajen ganin an zabi su Sanata Lawan, a a, har  da ’yan Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar APC na kasa baki daya da dukkan gwamnonin jam’iyyar da duk wani mai ruwa-da-tsaki na jam`iyyar a kasa da jihohi, duk sun dage wajen ganin baki ya zo daya wajen zaben wadannan mutum biyu, a zaman shugabannin majalisun biyu.

Hakan kuwa ta tabbata a ranar Larabar makon jiya da aka kaddamar da majalisun dokokin biyu a karon farko, kusan dukkan wadancan masu ruwa-da-tsaki na Jam’iyyar APC da na ambata sun halarci taron kaddamarwar da kuma zaben shugabannin majalisun biyu, don tabbatar da cewa gwanayensu sun haye.

Ba ko shakka hakan ta sa Sanata Ahmed Lawan ya samu nasarar zama Shugaban Majalisar Dattawa da kuri’a 79, yayin da abokin karawarsa Sanata Ali Ndume (APC daga Jihar Borno) da ya dage a kan sai ya yi takarar ya samu kuri’a 28, kuri’un da ake zargin akasarinsu ’ya’yan Jam’iyyar PDP ne suka kada masa su. Shi ma Sanata Omo-Agege (APC daga Jihar Edo), ya yi nasarar zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan da kuri’a 68, a kan abokin karawarsa na Jam’iyyar PDP kuma tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Ike Ekweramadu da ya samu kuri’u 37. A can Majalisar Wakilai Honorabul Gbajabiamila shi ya yi nasarar zama Shugaban Majalisar Wakilai da kuri’a 281 a kan abokin karawarsa Honrabul Umar Bago (APC daga Jihar Neja) da ya samu kuri’a 76. Honorabul Ahmed Idris Wase (APC daga  Jihar Filato), ya samu zama Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai ba hamayya.

Kodayake siyasar wannan zamanin ta zama kasuwar bukata, ba ta akida  ko halacci ba ce, don kuwa da ta akida ko halacci ne, da ba a rika samun raba-rana ba a tsakanin yaro da ubangida a jihohi irin su Kwara da Sakkwato da Kano da Borno da Legas da  sauransu ba tunda aka faro wannan jamhuriyyar a 1999, yau shekara 20, ba kakkautawa.

In ba don wadancan abubuwa na bijirewa da aka rika samu ba, sai ka bugi kirji ka ce babu wani sabani da za a samu tsakanin Bangaren Zartarwa  da na Dokoki a wannan karon, bisa ga la`akari da irin yadda bangaren dokokin ya dage a kan lallai sai wadannan shugabanni za su shugabanci majalisun dokokin.

Mai yiwu wa da tunanin haka a cikin zuciyarsa, ta sanya a cikin sakonsa na taya murna ga wadanda aka zaba aka ji Shugaba Buhari yana cewa “Ko kusa ba ya fatar majalisun dokokin su zama ’yan amshin Shata ga Bangaren Zartarwa.” Shi ma Sanata Lawan an ji shi yana cewa da yardar Allah, za su rika zartar da kasafin kudin kasar nan na kowace shekara a cikin watanni uku, muddin Bangaren Zartarwar zai rika mika musu Kasafin Kudin a tsakanin watan Satumba zuwa Oktoban kowace shekara. Zartar da Daftarin Kasafin kudin kasar nan da majalisa ta 8, ta rinka yi bayan wata shida zuwa bakwai, ya yi ta haddasa sabani tsakanin bangarorin mulkin biyu da kawo koma baya cikin yin ayyukan raya kasa a kasar baki daya.

Saura da me? Yanzu ’yan kasa za su zuba idanu wajen bibiyar irin zaman da za a yi tsakanin bangarorin biyu, wala’alla ko za a samu canji, ko kuma za a gwammace jiya da yau. Idan dai har bangarorin biyu suka kasa tabuka komai da zai fitar da talakawan kasar nan daga cikin irin kancin rashin zaman lafiya da sukurkucewar matsalolin tsaro, matsalolin da suke kara haddasa fatara da talauci da rashin ayyukan yi da ma rashin gudanar da ayyukan raya kasa da za su kara bunkasa rayuwar ’yan kasa, to, kuwa talakawa na iya cewa ba su ga abin da mulkin dimokuradiyya ya tsinana musu ba. Da yardar Allah, mulkin dimokuradiyya ya kankama a kasar nan, ya rage ga masu tafiyar da shi su rika sa tsoron Allah a cikin zukatansu kan yadda abin da za su yi. Allah Ya kama musu amin summa amin.