✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marar hannu ta zama kwarar direbar motar tasi

Wata mata mai `ya `ya biyu mai suna Janet Brown da aka haifa da rashin yatsun hannuwa da kafafu mai shekara 31 a jihar North…

Wata mata mai `ya `ya biyu mai suna Janet Brown da aka haifa da rashin yatsun hannuwa da kafafu mai shekara 31 a jihar North Carolina kasar Amurka tana kokarin yi wa kanta hidindimun  da take bukata har da sana`arta wanda ya zama dole tayi amfanin da hannu wato tukin mota.

Janet dai tana sana`ar tukin mota ne inda ta zama kwararra a fannin don ciyar da iyalanta, tana wannan sana`ar ne da safe yayin da `ya `yanta biyu ke makaranta.

Fasinjojin Janet, ya nada wuya su fahimci yadda take tuki da hannu ba yatsu kuma har ta iya juya sitiyarin motar da canza giyar motar. Ba wai yatsun hannun ne kawai Janet ba tada shi, har da mafi yawan yatsun kafarta, sai dai ta kan yi kokarin sanya budadden takalmi.

Don farantawa sauran jama`a  masu nakasa, Janet ta kaddamar kungiya mai zaman kanta da hadin gwiwar kungiyar Helping Hands, don kara masu kwarin gwiwa da ilmantar da duniya game da jama`a masu nakasa.

Janet dai nada kudirin nunawa jama`a cewa, wadanda suke da nakasa ba abin kyama bane, kuma masu nakasar bai kamata su boye wa jama`a yanayin yadda suke gudanar da rayuwarsu.

Janet ta ce, duk da irin nakasar da take tare da ita na rashin yatsu, ba zata iya cewa ita nakasassiya bace. Saboda tana iya yin ayyukanta na yau da kullum. A cewar Janet larurrata bai hana ni yin komai ba. Mafi yawan fasinjojin da nake tukawa sun amince dani cewa ni kwararriyar direba ce, wasu har so suke in zamar masu direba ta musamman. Sai dai mafi yawan jama`a suna ganin masu nakasa mabukata ne, suna bukatar taimako, amma anan ba haka abin yake ba.

Janet ta kara da cewa, wasu lokutan mutane na kokarin taimakamin, sai su rika tunanin bazan  iya yi wa kaina kome bane. A zaton jama`ar na samu nakasa ne hanyar mummunan hadari.

“Ba za a iya mun tunanin ko sanadiyyar hadari bane yasa na rasa `yan yatsu na, an haife da wannan larurar ne, wasu na tunanin babu mai taimaka min ne. Zan so ace an  tambaye ni ba wai a yi min zato ba. Duk mai son karin bayani ni zai tambaya”.

Janet ta kan fadawa `ya `yanta cewa kamanninta ya banbanta da sauran iyaye mata, amma duk da haka tana iya yin abin da sauran iyaye zasu yi. Don haka ta hada gwiwa da kungiya mai zaman kanta ta Helping Hands, da fatan taimakawa wasu mabukata.