✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marayu 1000 suka samu tallafin Maigemu a Kankiya

A ranar Asabar da ta gabata ce Gidauniyar Maigemu ta kaddamar da rabon kayan Sallah ga yara marayu su dubu daya, wadanda aka zabo daga mazabu…

A ranar Asabar da ta gabata ce Gidauniyar Maigemu ta kaddamar da rabon kayan Sallah ga yara marayu su dubu daya, wadanda aka zabo daga mazabu goma na Karamar Hukumar Kankiya, a Jihar Katsina.

Taron wanda ya gudana a dakin taro na Shema Sport Centre da ke cikin garin Kankiya, ya samu halartar mutumin da ya assasa gidauniyar, Alhaji Salisu Hamza Rimaye, dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Karamar Hukumar Kankiya.

A jawabinsa, shugaban gidauniyar, Malam Saddik Ya’u ya bayyana cewa an yi kokari matuka wajen ganin cewa wadanda suka fi cancanta ne aka zabo, domin ba duka maraya ne ke da bukatar irin wannan taimakon ba. Ya kara da cewa a bara yara 500 ne suka amfana da shirin amma a bana aka kara yawansu zuwa 1000 saboda lura da irin yadda shirin ya yi tasiri a baya.

A nasa jawabin, shugaban taro, tsohon Gwamnan Mulkin Soja na Jihar Borno, Kanar Abdulmumini Aminu mai ritaya, ya yi kira ga dukkan jama’a da su yi koyi da wannan aikin alherin da Alhaji Hamza Rimaye ke gudanarwa. Ya kuma jawo hankalin marayun da suka amfana da cewa idan suka dage suka yi karatu kuma suka yi aiki tukuru, su ma wata rana suna iya zama kamar Maigemu.

Shi ma a nasa jawabin, Maigemu, Alhaji Salisu Hamza Rimaye ya jaddada godiyarsa ga Allah da a cikin iko da hukuncinSa Ya ba shi damar gudanar da irin wadannan ayyuka. Ya kara da cewa wannan aikin an dade ana yinsa amma dai ba a fara bayyana shi duniya ta sani ba sai daga bara. Ya ce an fara bayyanawar ne domin hakan ya zama kira ga sauran masu hali su ma su shigo cikin irin wannan aikin, “musamman saboda lura da irin tsananin halin bukata da wasu daga cikinmu suke. A bana ba dinkin Sallah kadai za a raba ba, an tanadi masara buhu dari domin rabawa ga wadanda suka fi bukata a cikin al’umma, domin su ma su samu su yi abincin Sallah.”

Mutane 300, mabukata 30 daga kowace mazaba ne suka samu masarar, inda kuma gidauniyar ta samar da Naira 300,000, aka ba kowannensu Naira dubu daya, kudin cefane.

Taron ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen Karamar Hukumar Kankiya da suka hada da babban bako na musamman, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Alhaji Tasi’u Musa Maigari da Alhaji Isa Ali Bindawa da Alhaji Nasiru Yahaya Daura da Kantmomin riko na kananan hukumomin Kankiya da Kusada, Alhaji Musa Maikudi Kankiya da Alhaji Sama Mati da Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Kankiya, Malam Junaidu Abdul’aziz Rimaye da Shugaban Kwalejin Kiwon Lafiya da ke Kankiya, Alhaji Tanimu Master da Ma’ajin Jamiyyar APC na Jihar Katsina, Alhaji Yusuf Kankiya.

Sauran manyan bakin sun hada da Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Kankiya, Alhaji Danjuma Mamman Rimaye da Alhaji Ashiru Hamisu Usman Magama, wanda ya wakilci babban mai kaddamarwa Arc. Ahmad Musa Dangiwa sauran manyan malamai da wakilan Hakiman Kankiya da Rimaye.