✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Martani ga Kungiyar Dattawan Arewa

Assalamu alaikum. Da fatan dukan ma’aikatanku suna cikin koshin lafiya. Na shigo wannan fili ne don in yi martani a kan janye goyon baya da…

Assalamu alaikum. Da fatan dukan ma’aikatanku suna cikin koshin lafiya. Na shigo wannan fili ne don in yi martani a kan janye goyon baya da Kungiyar Dattawan Arewa ta yi ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben bana.

To mu dai ’yan Najeriya muna son sanar da ’ya’yan wannan kungiya cewa, wannan mataki sun dauka ne a karan kansu, amma ba da yawun mu al’ummar yankin Arewa ba. Domin mu yanzu ne ma muke kara son Buhari, kuma muke fatan Allah Ya nuna mana yadda a bana za mu ba shi kuri’u fiye da wanda muka ba shi a shekarar 2015. Saboda ba za mu taba zama “Kaza ci ki goge bakin ki ba,” musamman idan aka yi la’akari da yadda Shugaban Kasa yake iya kokarinsa wajen ganin an kawo karshen ta’addanci a wannan kasa, wanda a baya ya hana kusan daukacin ’yan Arewa barci da ido biyu rufe. Don haka yanzu ne muka fara son Baba Buhari.

Daga Isah Ramin Hudu Hadeja. 08060353382