✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masana sun shata hanyoyin samar da zaman lafiya a Katsina

A wani yunkuri na samar da zaman lafiya da ingantattar zamantakewa cikin al’umma a Jihar Katsina, kungiyar KbC ta shirya wata gagarumar bita wadda ta…

A wani yunkuri na samar da zaman lafiya da ingantattar zamantakewa cikin al’umma a Jihar Katsina, kungiyar KbC ta shirya wata gagarumar bita wadda ta hada masana da shugabannin al’umma, wadanda suka shata hanyoyi da matakan da za su tabbatar da zaman lafiya mai dorewa ba a Jihar Katsina ba kadai, har ma da Najeriya baki daya.

Taron, wanda ya gudana a ranar Lahadin da gabata, an gudanar da shi ne a dakin taro na Dallatu da ke Soli Centre, cikin birnin Katsina; inda masana suka gabatar da takardu daban-daban game da matakan samar da zaman lafiya.

Da yake bayyana sakamakon bitar, shugaban Kwamitin Tattara Bayanan taron, Dokta Shamsuddin Bello ya ce domin tabbatar da samun zaman lafiya cikin al’umma, taron bitar ya ce sai an dauki matakai kamar haka: “A ba sarakunan gargajiya damar gudanar da mulki ta hanyar karfafa ikonsu a gwamnatance, kasancewarsu mafi kusa da al’umma. A samar da ayyuka da sana’o’i ga al’ummar Jihar Katsina. A ba harkar ilmi kulawa ta musamman, ta hanyar daukar kwararrun malamai da wadatuwar kayan duk da ake bukata a yayin koyarwa.”

Sauran matakan, a cewar takardar bayan taron sun hada da: “Wayarwa da fadakarwa da ilmantar da daukacin al’umma lokaci zuwa lokaci a kan amfanin zaman lafiya. A samar da mulkin adalci daga shugabanni zuwa wadanda suke jagoranta. Al’umma su rika yi wa dokokin kasa biyayya. ’Yan siyasa su rika mutunta dokokin kasa. Al’ummar da ke zaune wuri daya su gano bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su kuma fahimce su. ’Yan jarida da sauran kafafen sadarwa suna da rawar takawa wajen dorar da zaman lafiya da kawo ci gaba mai ma’ana ga al’ummar Jihar Katsina.”

Malam danjuma Katsina, wanda shi ne jagora kuma shugaban shirya wannan bita baki daya, ya tabbatar da cewa za a ci gaba da irinta da nufin tabbatar da zaman lafiya ga al’ummar Jihar Katsina ba tare da gajiyawa ba.

Kadan daga cikin mahalarta tattaunawar sun hada da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, wanda Farfesa Badamasi Abbas Charanci ya wakilta, Mai martaba Sarkin Katsina wanda ya samu wakilcin Alhaji Aminu Mamman Dee. Cikin masana kuwa, taron bitar ya samu halartar Dokta Musa Muhammad Jibiya, Dokta Aminu Garba Waziri, Dr. Muttaka Rabe Darma da Dokta Bashir Abu Sabe, Dokta Jibrin Hussaini, Dokta Aliyu Muri, Dokta Shamsuddin Bell, Babangida Nasamu da sauransu da dama.