✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Dass ta nada Galajen Dass na farko

Majalisar Masarautar Dass da ke Jihar Bauchi ta nada Alhaji Nuhu Muhammad Bashi a matsayin Galajen Dass na farko. Da yake nada masa wannan Sarautar,…

Majalisar Masarautar Dass da ke Jihar Bauchi ta nada Alhaji Nuhu Muhammad Bashi a matsayin Galajen Dass na farko.

Da yake nada masa wannan Sarautar, Mai Martaba Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu Usman ya bayyana cewa “Galajen ya nuna halin dattako kuma ya zauna lafiya da jama’arsa lokacin da yake rike da sarautar mai gundumar Shalgwantar kafin a soke sabbin sarautu da aka nada, kuma ya zauna lafiya da masarautar, kuma ya yi kyakykyawan jagoranci shi yasa muka sake karramashi da sarautar Galajen Dass na farko.” 

daga nan sai ya hori jama’ar kasarsa da su kara kokari wajen zama lafiya da juna kuma su yawaita adduoi domin samun zama lafiya da karuwar arziki a masarautar, jiha da kuma kasa baki daya, sannan ya bukaci sabon Galajen da ya rike mukaminsa da gaskiya da adalci ya kuma yi masa addu’ar  Allah Ya taimakeshi riko. 

Daga bisani sai aka raka sabon Galajen da kade-kade da bushe-bushe inda ya zaga cikin garin Dass, ya kuma zarce zuwa gidansa inda ya karbi gaisuwar mubaya’a daga al’ummar masarautarsa da kuma ’yan uwa da abokan arziki.

Da yake jawabi, sabon Galajen Dass din, Alhaji Nuhu Bashi, godiya ya yi wa mai Martaba Sarkin Dass saboda wannan karamci da ya masa. ya kuma yi alkawarin ci gaba da bada gudummawarsa domin ci gaban masarautar Dass, sannan ya nemi jama’a da su taya shi da addu’a kuma su bashi cikakken goyon baya domin samun nasarar ayyukansa