✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Kaltungo ta nada Mista Seni James Barka Wakilin Makaranta

A ranar Asabar din makon jiya ne mai Kaltungo Injiniya Saleh Muhammad, ya nada Shugaban Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Jihar Gombe da ke garin Kaltungo,…

A ranar Asabar din makon jiya ne mai Kaltungo Injiniya Saleh Muhammad, ya nada Shugaban Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Jihar Gombe da ke garin Kaltungo, Mista Seni James Barka, a sarautar Wakilin Makaranta na Kaltungo.

Mista Seni James Barka, baya ga kasancewar sa Shugaban Kwalejin

Kimiyyar Lafiyar, kwanan nan ne aka zabe shi ya zama Shugaban

Makarantu da Kwalejojin Lafiya ta Najeriya kasancewarsa kwararre kuma masanin kiwon lafiya.

Da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa a garin Kaltungo, Wakilin Makarantar ya bayyana cewa ya jima yana aiki da hukumomin lafiya irin su Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a bangaren rigakafin shan-inna da sauran wurare da dama.

Ya ce ganin yana aiki da bangaren lafiya ne kuma shi ne Shugaban Kwalejin Kimiyyar Lafiyar, ya sa Mai martaba Sarkin Kaltungo Injiniya Saleh Muhammad, ya nada shi Wakilin Makarantar Kaltungo don ganin an ciyar da harkar ilimi a yankin Kaltungo.

Mista Seni Barka, ya gode wa Mai Kaltungo bisa wannan nadi da ya yi masa da kuma irin hadin kan da ya bayar har aka daga martabar makarantar daga Makarantar Koyon Aikin Lafiya zuwa Kwalejin Kimiyyar Lafiya.

Ya ce a fadar Mai Kaltungo yana da rawar takawa kamar kowane Basarake musamman a bangaren abin da ya shafi yadda za a rika samar wa ’ya’yan yanki damar shiga makarantun gaba da sakandare a fadin kasar nan.

“A sarakunan da aka yi a Masarautar Kaltungo, ba a samu Sarkin da ya ciyar da masarautar gaba ba irin Injiniya Saleh Muhammad,” inji Wakilin Makarantar.

Ya ce cikin irin hidimar da mai din yake yi don ganin yankin Masarautar sa ta ci gaba wani lokacin shi da Mai Martaba suna takawa kauyuka da kafa musammam ma wani kauye da ake kira Galdimaru da Gwandum,  don ganin irin halin  da talakawansa suke ciki.

Ya kara da cewa, Mai Kaltungo yana iya bakin kokarinsa wajen hada kan al’ummar Kaltungo don a zauna lafiya haka suma talakawan suna ba shi hadin kan da ya kamata.

A matsayin sa na wakilin Makarantar Masarautar yace zai sake hada kai da mai Kaltungo, don ganin an bunkasa asibitin macizai na garin Kaltungo wanda yake kula da jihohin arewa maso gabas da Abuja da Jigawa da Jos.

Ya ce ciyar da asibitin gaba zai taimaka wa daliban da suke karatu a kwalejin sanin yadda ake hada magani saran Macizai da kula da mai raunin saran macizan.

Ya ce zai hada kai da Mai Kaltungo da sauran sarakunan yankin don ganin an shawo kan matsalar rashin samun shigar yaransu a makarantu yadda ya kamata.

Kafin nadin Seni James Barka, Wakilin Makarantar Kaltungo shi ne Tafarkin Gwandun a Karamar Hukumar Shongom.