✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mashayi ya hadiye mabudin gida a mashaya bayan ya bugu

A makon jiya ne wani matashi mai suna Chang daga yankin Guangdong a kasar China ya ziyarci asibiti sakamakon mummunan ciwon kirji da yake fama…

A makon jiya ne wani matashi mai suna Chang daga yankin Guangdong a kasar China ya ziyarci asibiti sakamakon mummunan ciwon kirji da yake fama da shi, bayan biciken likitocin asibitin sun sanar wa matashin cewa, yana fama da ciwon da ke damunsa ne sakamakon hadiye mabudin gida da ya yi.

Chang ya ce ya yi tunanin cewa, ya batar da mabudin ne kafin ya ziyarci mashaya tare da abokansa a daren ranar.

Chang, mai kimanin shekara 26, ya ziyarci mashayar ce da abokansa don bikin zagayowar ranar hutun mako, kuma da ya koma gida cikin tsakar dare ya rika dube-daben mabudin amma bai gan shi ba, har sai da ya nemi wurin kwana a wajen wasdansu.

Wannan matashin mai shaye-shaye bai san ya hadiye mabudin ba don haka ya wuce kai-tsaye ya nufi dakin da zai kwana. Bayan gari ya waye sai ya fara jin ciwo a jikinsa sakamakon giyar da ya sha da matsanancin ciwon kirji hakan ya sa ya je asibitin Dongguan don duba lafiyarsa.

A lokacin da likitoci suka sanar da sakamakon binciken da suka yi ta amfani da na’urar daukan hoton jikin mutum D-ray, sai suka gano wani karfe mai kama da mabudi a cikinsa. Likitocin sun tambaye shi yadda aka yi mabudin ya shige masa ciki, sai ya ce akwai lokacin da ya batar mabudinsa da daddare amma ya ki yin bayanin yadda aka yi hadiye mabudin .

A cewar kafar labarai ta Sohu da ke China, ta ce Chang ya yi matukar mamakin abin da likitocin suka gani a cikinsa.

Ma’aikatan Asibitin Dongguan, sun bayyana mamakin yadda aka yi har aka hadiye mabudin ya zauna a cikin dan Adam, sun bayyana hakan a matsayin ganganci ga rayuwa. Ganin karfe na iya farka hanji. Kuma lokacin da ake yunkurin ciro karfen ya cutura har sai da aka yi amfani da hikima wajen yin tiyatar gaggawa.

Dokta Zhang Yuyu, ya bayyana wa manema labarai cewa, da farko sun yi amfani da na’urar gano abin da ke cikin dan Adam amma suka fuskanci kalubale wajen ciro mabudin, saboda yadda mabudin ya makale abin kamar ba zai  yiwu ba, sakamakon abin da zai biyo baya bayan tiyatar.

Ranar da likitocin suka ware don yi wa Chang tiyata ta yi daidai da ranar da gwamnati ta ware don yin hutun ma’aikata. Mataimakin Daraktan Gudanarwar asibitin na daga cikin wadanda suka taimaka aka yi tiyatar gaggawar.

A karshe likitocin sun yi nasarar ciro mabudin da wasu abubuwan da Chang ya hadiye a cikinsa.