✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu coronavirus a Najeriya sun haura 15,000

Mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 15,181 bayan karin mutum 627 sun kamu da cutar a jihohi 23. Haka kuma…

Mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 15,181 bayan karin mutum 627 sun kamu da cutar a jihohi 23.

Haka kuma yawan wadanda suka warke daga cutar a Najeriya ya karu zuwa 4,891 a jihohi 35 da kuma Abuja.

Alkaluman Hukumar Yaki da Cutttuka Masu Yaduwa (NCDC) na ranar Juma’a 12 ga watan Yuni sun nuna mutum 9,891 ne suka rage dauke da cutar a Najeriya.

Ta kara da cewa zuwa ranar an yi wa mutum 88,432 gwajin cutar wadda ta yi ajalin mutum 399 a kasar.

Jihohin da aka fi samun bullar cutar a ranar su ne Lagos-229, Abuja-65, Abia-54, Borno-42 da kuma Oyo-35.

Jihohin mafiya wayawan masu cutar coronavirus a Najeriya su ne Legas-6,840 da Abuja-1,162 sai kuma Kano-1,049.