Da Dumi Dumi

Masu damfarar yin kudi da tantabara sun shiga hannu a Katsina

Dubun wasu ‘yan damfara ta cika yayin da suka fada komar ‘yan sanda. Mukaddashin Kakakin ‘yan sandan Jahar Katsina, Mataimakin Sufuritanda Anas Gezawa ne ya gabatarwa manema labarai wadannan matasa su uku a Hedkwatar ‘yan sandan da ke nan Katsina.

Wadanda aka kama sun hada da: Ayemojuba Dada, Ogun Moriti da Ojuolape Akin. Duk kansu daga Jahar Ogun, wani mai suna Chinedu Onaja, ne ya kawo koken a sashen rundunar mai yaki da miyagun laifuka a yau Alhamis inda suka karbi tsabar kudi har sama da Naira dubu 90 da sunan zasu mayar da shi wani hamshakin mai kudi wanda duniya zata san shi kamar su Dangote.

Su dai wadannan ‘yan damfara suna aiki ne da wasu irin kayayyakin yin sihiri da suka hada da wasu gumakan roba, farin yadi, diram da wasu layu gami da wata kwarya wadda aka zubawa wani abu mai kama da manja da wani gari da karamin icce da gawar wasu tantabaru 2 da kuma wata farar tantabara mai rai da sauran kayan da ke nuna alamun yin sihiri.

Wadanda ake zargin sun ce sun yi kamar wata guda a cikin garin Katsina a Unguwar Kofar Sauri. Chinedu ne mutun na farko da suka fara jaraba aikinsu akansa wanda suka yi masa Dalar Amurka don ganin tabbas. Sun nemi ya basu Naira milyan uku da rabi don mayar da shi mai kudin da zai kamo su Dangote.

Mukaddashin Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce, suna ci gaba da bincike akan su wadannan ‘yan damfarar da basu musanta zargin da ake yi masu a lokacin suke yi wa manema labaran bayanai a lokacin da aka tuntube su ba.

ADVERTISEMENT
Share