✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa sun kashe jami’in DSS a Jihar Katsina

Masu ta’adar garkuwa da mutane sun kashe wani jami’in hukumar tsaron ta farin kaya (DSS), Sadiq Abdullahi Bindawa, a jihar Katsina. Marigayi Sadiq ya yi…

Masu ta’adar garkuwa da mutane sun kashe wani jami’in hukumar tsaron ta farin kaya (DSS), Sadiq Abdullahi Bindawa, a jihar Katsina.

Marigayi Sadiq ya yi gamo da karshensa a hannun ‘yan ta’addan bayan sun karbi naira miliyan 5 na kudin fansa ta garkuwar da suka yi da shi.

Tun da farko lamarin ya faru ne a ranar Asabar yayin da masu garkuwar suka kai masa takakakka awanni kadan bayan shigarsa gida yayin da ya tafi hutun karshen mako daga Abuja zuwa Katsina.

Maharan sun yi awon gaba da shi sannan kuma suka bukaci naira miliyan 25 a matsayin kudin fansa.

Abokan aikin mamacin sun yi wa masu garkuwar kwanton bauna a inda suke shirin karbar kudin fansa, lamarin da ya janyo musayar wuta a tsakaninsu.

A yayin da a nan ajali ya cimma wasu daga cikin masu garkuwar, ‘yan kalilan da suka tsere suka koma suka harbe Sadiq tare da barin gawarsa a dokar daji.

Majiyarmu ta ce an yi jana’izarsa a safiyar yau ta Talata bisa koyarwar addinin Islama.