✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu magani sun sami wata kasuwar a Kano

Masu harkar sayar da magunguna a Kasuwar Sabon Gari da ke Kano za su koma sabuwar kasuw da suka samar wa kansu

Kungiyar masu sayar da magani a Kano ta bayyana ta ce sun samu wata sabuwar kasuwar da za su koma, su bar Kasuwae Sabon Gari.

Shugaban kungiyarsu, Musbahu Yahaya Khalid ya ce komawarsu aabuwae kasuwar za ta kawo karshen halin damuwa da suka shiga.

Ya bayyana haka ne a yayin da suka kai wata ziyarar duba kasuwar wacce take a Filin Dalar Gyada da ke Karamar Hukumar Dala a birnin Kano.

A cewarsa zabin da suka yi na Kasuwar Dalar Gyada ya biyo bayan sahalewar Gwamnatin Jihar Kano, don su tashi daga inda da suke a Kasuwar Sabon Gari.

A cikin watan Fabrairu ne hukumar kula da magunguna ta kasa (PCN) tare da hadin gwiwar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna (NAFDAC)  suka rufe shagunan masu ’yan maganin da ke rukunin kantinan zamani na Malam Kato da kuma Mai Karami Plaza a Kasuwar Sabon Gari, da nufin tilasta ’yan maganin komawa shagunan da aka tanada musu a Kasuwar Dangwaro da ke kan babban titin Zariya.

Hukumomin sun dauki matakin ne bayan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Kano karkashin jagorancin Mai sharia A. T Liman ta yi, inda ta umarci ’yan maganin su koma Kasuwar Dangwaro.

Wasu daga cikinsu suka koma can, amma yawancin sauran sun yi biris da umarnin na kotu.

Shugaban, ya kara da cewa sabon wajen da suka samu ya fi na Kasuwar Dangwaro saboda hayar shagunan ta fi arha sannan yawan shagunan ya fi na Dangwaro.

“Mun gamsu da wannan wuri da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana da ‘Cibiyar Magani ta Kano saboda ta fi ta Dangwaro.

“Shaguna Dangwaro ba su fi 600 ba amma na wannan kasuwar sun fi 5,000 wanda na tabbata za su ishi membobinmu,” in ji shi.

Ya kuma ce an ba su wa’adin watanni biyu su kwashe kayansu daga Sabon Gari zuwa sabuwar kasuwar ta Dalar Gyada.

A cewarsa a ksuwar an tanadi ofisoshin ’yan sanda da na NAFDAC da na PCN domin su rike sa ido game kan harkokin da ake gudanarwa a kasuwar.

“Mun sanar da ofisoshin Hukumomin NAFDAC da PCN da na ’yan sanda saboda su rika bibiyar abin da muke yi.

“A matsayinmu na kungiya za mu ba su hadin kai wajen ganin an bankado asirin duk wani dan kasuwa da ke sayar da jabun magani ko muggan kwayoyi a kasuwar,” in ji shi.