✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu son Birtaniya ta fita daga Tarayyar Turai ’yan wuta ne – Shugaban EU

Shugaban Kungiyar Tarrayar Turai, Donald Tusk ya bayyana wadanda suke so Birtaniya ta fice daga Tarrayar Turai ba tare da wani kyakkyawan shiri ba a…

Shugaban Kungiyar Tarrayar Turai, Donald Tusk ya bayyana wadanda suke so Birtaniya ta fice daga Tarrayar Turai ba tare da wani kyakkyawan shiri ba a matsayin “’yan wuta.’’

Ya bayyana haka ne bayan tattaunawarsu da Ministan Ireland Leo Baradkar a Brussels.

Ya ce Tarrayar Turai za ta matsa lamba a kan yarjejeniyar barin iyakar kasar Ireland a bude ko da kuwa akwai batun ficewar Birtaniya domin a samu zaman lafiya.

Amma Mista Tusk da kuma Mista Baradkhar suna da shirin ko-ta-kwana a kan batun ficewar Birtaniya daga Tarrayar Turan.

’Yan Majalisar Dokokin Birtaniya irin su Andrea Leadsom tuni suka fara mayar da martani a kan wadannan kalamai na Mista Tusk.

Misis Leadsom, wadda tana daya daga cikin wadanda suka yi ta kiraye-kirayen ficewar Birtaniya, ta bayyana kalaman a matsayin “kalaman da-na-sani’’ kuma ‘“kalaman da ba za su taimaka ba.’’

’Yar majalisar, wadda kuma ’yar Jami’iyyar Conserbatibe ce ta shaida wa BBC cewa Tusk “ba ya da da’a.’’

A kwanakin baya ne ’yan Majalisar Dokoin Birtaniya suka fitar da wasu sababbin shawarwari domin sauya makomar kasar a kan batun ficewarta daga Tarayyar Turai da ake kira Bredit.