✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata Musulmi za su yi gangamin Ranar Hijabi ta Duniya

Gamayyar Kungiyoyin Mata Musulmi na Najeriya sun shirya tsaf domin gudanar da gangami Ranar Hijabi ta Duniya karon na bakwai a gobe Asabar a Birnin…

Gamayyar Kungiyoyin Mata Musulmi na Najeriya sun shirya tsaf domin gudanar da gangami Ranar Hijabi ta Duniya karon na bakwai a gobe Asabar a Birnin Tarayya Abuja.

Ana gudanar da gangamin ne a duk fadin duniya ranar 1 ga Fabrairun kowace shekara domin sauya tunanin da wadansu ke yi ga masu sanya Hijabi a cikin al’umma tare da nuna muhimmancin sa Hijabin ga mata Musulmi a zaman abin da ke nuna kamalar mace.

Da ta jagoranci ayarin gamayyar zuwa suka Hedkwatar Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya, Shugabar Sashen Hulda da Jama’a ta Gamayyar, Barista Rukayya Sabi’u Dindi ta ce taken gangamin na bana shi ne “Hadin Kai Cikin Bambance-Bambance” wanda ciki za a tattauna batun saka hijabi tare da nuna cikakken ’yancin da mai saka shi take da shi a cikin jama’a.

Ta yi kira ga hukumomin gwamnati da sauran kafofi masu zaman kansu da su kalli hijabi a matsayin abin da ke nuna bambance-bambance da hadin kai tare da zaman lafiya a tsakanin jama’a. Ta nuna cewa, saka hijabi na nuni ga addinin Musulunci addini ne na zaman lafiya wanda bai kamata a nuna kyama gare shi ba. Gamayyar ta kuma yi tir da abin da ta kira nuna kyama ga masu saka hijabi a wasu sassan duniya da aka fuskanta a bara, inda ta ce ko a nan Najeriya hakan ya faru a wasu yankunan kasar nan, inda aka hana wadansu ’yan mata shiga aji su dauki darasi saboda kawai sun saka hijabi. Ta ce sun yi na’am da sam barka da matakin da Hukumar NYSC ta yi na barin mata Musulmi su sanya kananan hijabai a sansanonin horar da masu yi wa kasa hidima. Amma sun bukaci  Hukumar NYSC ta kyale mata su rika amfani da dogon buje, maimakon saka wando a sansanonin.

Sun yi kira ga hukumomin tsaro na kasar nan su yi koyi da Hukumar NYSC wajen sauya yunifom dinsu domin bai wa mata Musulmi masu sha’awar shiga harkar damarar damar neman aikin.

Ranar Hijabi ta Duniya dai ana gudanar da ita ce kowace shekara bayan da wata mata mai suna Nazma Khan ta assasa ta a shekarar 2013.