✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matan aure biyu sun yi musayar mazansu a Kenya

Wadansu matan aure biyu a Karamar Hukumar Busia da ke  kasar Kenya sun yi musayar mazansu, don kawai su samu annashuwa da zaman lafiya. Daya…

Wadansu matan aure biyu a Karamar Hukumar Busia da ke  kasar Kenya sun yi musayar mazansu, don kawai su samu annashuwa da zaman lafiya.

Daya daga cikin matan mai suna Lilian Weta mai shekara 28, mahaifiyar ’ya’ya uku ce, sai kuma daya matar mai suna Millicent Auna mai shekara 29 wanda ita ma ta taba haihuwa, sun yanke shawarar sauya mazansu ne a tsakaninsu don samun farin ciki kamar yadda suka ce.

Millicent Auma, tana tare ne da mijinta mai suna Christopher Bwire a kauyen Siroba da ke yankin Matayos, inda ta rabu da mijin ta koma wajen mijin Lilian mai suna Kebin Barasa.

Lilian Weta wadda take tare da mijinta Kebin da suka yi aure sama da shekara 10 a garin Namwitsula  a yankin Butula kuma suka haifi ’ya’ya uku, suna yawan samun rashin jituwa da yawan fada a tsakaninsu.

Lilian, ta bayyana wa jaridar Standard Digital cewa, wata rana mijinta ya dawo gida da wata matar mai suna Millicent sai ya fada mata cewa ya yi sabuwar mata.

“Sun shigo cikin gidan da misalin karfe 1 na tsakar dare tare da Millicent, sai mijina ya ce, wannan daren na musamman ne ga matata,” inji Lilian.

Lokacin da Lilian ta tuntubi mijinta sai ya ce mata, ta je ta nemi mijin Millicent sannan ta aure shi. Kawai sai Lilian, ta fahimci sakamakon rashin jituwar da suke yi ne ya sa haka. Ta kara da cewa “An zo karshen rikicin da yake tsakaninmu,” kuma ta samu kwarin gwiwar barin tsohon mijinta a garin Matayos ta fara neman Christopher ido rufe.

“Mijina ya ce, min in tafi in nemi mijin Millicent da aure. Sai na tambayi mijin nawa cewa, zai ji dadi idan har zan auri mijin wanda ya kawo gida? Sai ya ce babu damuwa.”

Lilian, ta kira dan uwanta da ’yar uwarta ta bayyana masu abin da ke faruwa. Sai suka fada mata cewa, idan hakan zai haifar da zaman lafiya ta je ta auri wancan mijin.

Lilian, ta kara da cewa, ’yan uwana sun ba ni shawarar in aikata abin da mijina ya umarce ni da yi. Da safe na tafi wajen Christopher, na bayyana masa abin da ke faruwa a garin Butula.

Lilian ta bayyana wa Christopher cewa, “Millicent ta aure min miji, sannan sun ce in je in nema ka da aure.” Sai Christopher, ya bai wa Lilian umarnin ta je ta dauko ’ya’yanta uku ta dawo da su garin Matayos.

Christopher, ya amince zai ci gaba da zama da Lilian a matsayin miji da mata, bayan tsohuwar matarsa ta rabu da shi, bai san inda zai same ta a yanzu ba.

“Na kira Millicent lokuta da dama amma ba ta amsa kirana, sai kawai na yanke shawarar rabuwa da ita,” inji shi.

Christopher, ya kara da cewa a tsakaninsa da Kebin da suka yi musayar mata wani sai ya yi da-na-sanin daukar wannan shawarar. “Ko ni, ko shi, wani zai yi  nadama, amma ni dai a yanzu ina murna da faruwar haka,’ inji shi-.

Da aka tuntubi Kebin game da sabuwar matarsa sai ya ce, shi a yanzu haka bai bukatar Lilian saboda yana murna da sabon aurensa.